#Coronavirus: Ana ci gaba da gwajin ingancin ‘Chloroquine’ – FDA

0

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kira ga likitocin kasar su rika amfani da maganin zazzabi da aka sani mai suna Chloroquine domin warkar da coronavirus.

Trump ya ce hukumar Kula da Ingancin magunguna da Abinci ta kasar Amurka FDA ta tabbatar da ingancin abincin.

Sai dai kuma kwamishinan hukumar Stephen Hahn ya bayyana cewa akwai yiwuwar tabbaci chloroquine zainiya warkar da coronavirus, sai dai kuma ba a tabbatar da haka ba tukunna domin ana nan ana yin bincike akai.

“Bama so mu mutane su fada cikin zumudi da murnar haka da wiri wuri, sai mun tabbatar da ingancin sa.

NAJERIYA

Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa har yanzu babu tabbacin cewa maganin Chloroquine na maganin coronavirus.

Ya ce chloroquine da wani magani mai sun hydroxychloroquine na cikin magungunan da masana kimiya ke yin bincike a kai domin gano maganin coronavirus.

Har yanzu sakamakon binciken bai fito ba.

Mamora yace a kasar Faransa an gwada ingancin maganin chloroquine a jikin mutane 25 dake dauke da cutar inda bayan kwanaki shida sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna cewa coronavirus na nan a jikinsu.

Hukumar kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta ce ba a gama bincike akan wannan magani ba da tabbatar da ko yana maganin coronavirus.

WHO ta hada hannu da R&D Blueprint domin gano maganin cutar.

A yanzu dai chloroquine, maganin cutar kanjamau Kaletra, maganin mura favipiravir, da maganin cutar Ebola remdesivir na cikin magungunan da ake gudanar da bincike a kai.

Share.

game da Author