Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Akin Abayomi, ya ce akalla mutum 39,000 za su iya kamuwa da cutar Coronavirus, muddin jama’a ba su rika yin taka-tsantsan din kauracewa kusanci da juna ba.
Ya ce yi wa juna nesa-nesa ce hanya ta farko wajen dakile cutar Coronavirus a kasar nan, idan aka yi la’akari da yadda al’amurra suka rika kasancewa a sauran kasashen duniya.
“Ba wai ina mugun fata ba ne, amma dai idan aka dubi yadda cutar ke saurin yaduwa da watsuwa, mutum 39,000 na iya kamuwa a Legas, matsawar jama’a ba su rika yin nesa-nesa a tsakanin su ba.
“Amma idan aka rika kiyayewa, to duk rintsi wadanda za su kamu a Lagos ba za su wuce mutum 13 ba.”
Sai dai kuma Abayomi ya ce matsawar jama’a suka ki kiyayewa da bin dokokin da aka gindaya, musammam batun yin nesa da juna, cakuduwa wuri daya da sauran su, to majalisa za ta yi zaman gaggawa domin a kafa wasu tsauraran matakan da bai bayyana su ba.
Kwamishina ya ce dukkan wadanda suka kamu a Lagos, daga Turai suka dauko cutar, sauran da ba a can suka dauko ta ba Kuwa, duk a nan Lagos suka kamu da cutar sanadiyyar cakuduwa da wadanda suka dauko ta daga Turai.