Davido ya killace kansa bayan budurwar sa ta kamu da cutar coronavirus

0

Fitaccen mawakin zamani Davido ya bayyana cewa shima zai killace kansa bayan budurwarsa ta kamu da cutar coronavirus.

Mawakin ya sanar da haka ne a shafinsa na twitter ranar Juma’a.

Davido ya ce da shi da budurwar na sa Chioma da ‘yarsu karama na daga cikin mutane 31 da aka yi wa gwajin cutar inda sakamakon gwajin ya nuna cewa Chioma ce kadai ke dauke da cutar.

“Daga ni har Chioma mun yi tafiya zuwa kasashen waje. Bayan mun dawo ne muka Kai kanmu tare da duk wadanda muka yi mu’amula da su asibiti domin a yi mana gwajin cutar”.

Davido ya ce shima daga yanzu zai killace kan sa na tsawon kwanaki 14.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’a ne hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar cewa an samu karin mutane 16 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

A yanzu dai mutane 81 ne ke dauke da cutar , uku sun warke sannan daya ya mutu

Bayan haka gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga duk wadanda suka halarci bukin karrama jaruman fina-finai da aka yi su garzaya asibiti a duba su.

Ta ce bayan an kammala taron, an gano akwai wasu da suka kamu da cutar kuma suka hakarci wannan wurin taro.

Ali Nuhu, Ado Gwanja, Hassan Giggs, da Abubakar Mai shadda duk su halarci bukin.
.

Share.

game da Author