Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA Group, Abdulsamad Rabi’u, da wasu attajiran Najeriya sun bada gudunmawar biliyoyin nairori domin tallafawa gwamnati a yaki da yaduwar cutar coronavirus da take yi a Najeriya.
Wadanda suka bada irin wannan gudunmawa sun hada da Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Aliko Dangote
Jihohin da Rabiu ya ce za a raba kayan aikin musamman ga jami’an lafiya, sun hada da Lagos, Kano, Adamawa, Edo, Kwara, Rivers, Abia, Akwa-Ibom da kuma Sokoto, wadanda ya ce yawanci daga wadannan jihohi ne makaitakan kamfanonin sa suka fito.
Ya ce zai bayar da zunzurutun naira bilyan 1 ta hannun Babban Bankin Najeriya, CBN da kuma Kwamitin CBN da Kwamitin Shugaban Kasa Mai Yaki da Barkewar Cutar Coronavirus a Najeriya.
Kadan daga kayan da zai shigo da su, akwai: Takunkumin rufe fuska 100,000, rigunan kariyar kamuwa da cuta 100,000, safar hannu 1000, na’urorin gwaji 1000 da sauran su.
Haka kuma ministocin Najeriya sun sanar cewa za su bada rabin Albashin su na watan Maris domin tallafawa gwamnati a aikin yaki da yaduwar coronavirus da take yi. Ministoci 43 duka sun amince su yi haka.
Bankin UBA ta bada gudunmawar naira Biliyan 5, haka ita ma Polaris Bank, ta bada nata gudunmawar.
Cocin RCCG ta bada irin wannan gudunmawa.