CORONAVIRUS: Matakai 15 na wanke hannye domin kauce wa kamuwa -UNICEF

0

Hukumar UNICEF ta fitar da wasu matakai da kuma hanyoyin da ake bi wajen tsaftace hannaye, domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus.

Cikin wata muhimmiyar sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta kuma bayyana dalilan da ya sa ake kara matsin-lamba wajen wanke hannaye a lokutan annoba irin Coronavirus.

Dalilan Wanke Hannaye

1. An fi saurin kamuwa da cutar Coronavirus idan wata majina ta fito daga bakin mutum ko hancin sa ta diga a kan jikin sa. Ko kuma wata kwantsa ko hawaye sun fito daga Disamba idon mutum sun zuba a jikin sa.

2. Hannaye su ne ke yawan kai-kawo a jikin mutum, shi ya sa majina, ko wata kwantsa ko ruwan da ya fito a jikin mutum ya fi saurin shafar hannayen mutum.

3. Dalili kenan a irin wannan mawuyacin yanayi, ba a so mutum ya na yawan hangame baki ya na hamma, ko atishawa ko tari, ko kuma kakarin fitar da majina.

MATAKAN WANKE HANNAYE SABODA CORONAVIRUS

1. Da ruwa wanda ke kwarara a kan hannaye za a rika wanke hannu. Ba wai a tsoma hannayen a cikin wani ruwan da ke cikin wata roba ko kwano ba.

2. A yi amfani da sabulu sosai da sosai.

3. A rika cuccuda hannaye, a yi ana tsetstsefe yatsu da tsakankanin yatsun, da bayan hannu da kuma cikin farce.

4. A tarba hannayen a ruwa ana wankewa sosai da sosai.

5. Ana so mutum ya shafe akalla sekan 20 zuwa 30 ya na cuccuda hannayen sa tukunna.

6. Bayan an wanke hannaye, sai kuma a goge laimar da wani kyalle ko tawul mai tsabta, wanda mutum shi kadai ke rika amfani da shi.

7. Idan da sinadarin tsaftace hannaye za a wanke hannaye, wato hand sinitizer, shi ma sai an cuccuda din, kamar yadda ake wankewa da ruwa.

8. Ana wanke hannaye duk lokacin da mutum ya yi atishawa ko ya fyace majina ko kuma ya yi tari.

9. Ana wanke hannaye bayan an shiga cikin rintsin jama’a, kamar kasuwa, ko ma wane irin taro.

10. A na wanke hannaye bayan an taba kudi ko wani abu wanda ke da datti, ko wani abu da ya fito daga hannun wani.

11. Ana wanke hannaye kafin a ci abinci da kuma bayan an ci abinci.

12. A gaggauta wanke hannaye bayan shiga ban-daki.

14. A gaggauta wanke hannaye bayan taba shara, bola ko ma wani abu mai datti.

15. Kada a rika gajiya, kosawa ko nuna gandar kin wanke hannaye a kai a kai.

Hausawa sun ce, ‘idan kunne ya ji, to jiki ya tsira!’

Share.

game da Author