CORONAVIRUS: Taurin kan wadanda suka dawo Najeriya daga waje ne ya sa cutar ta yadu a Najeriya – NCDC

0

Babban Darakatan Cibiyar Kula da Cututtuka, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana laifin karuwar yaduwar cutar daga matafiyan da suka dawo ne daga kasashen da cutar ta Coronavirus ta yi muni sosai, saboda sun ki killace kan su, kamar yadda aka yi musu gargadi.

A wata hira da aka yi da shi a Litinin din nan da safe, a gidan talbijin na Channels, Ihekweazu ya ce babbar matsalar Najeriya ita ta ce masu dawowa daga kasashen waje.

Daga nan sai ya shawarci dukkan masu aiki a kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kan su su zauna su na aiki daga gidajen su.

Sannan kuma ya ce kowa ya yi kaffa-kafda da taka-tsantsan, domin nan gaba za a kara samun rahotannin wadanda suka kamu da cutar.

A ranar litinin aka samu karin wasu da suka kamu da cutar har 5. Sannan kuma mutum daya ya rasu da shima daga kasar Birtaniya ya dawo Najeriya makonni biyu da suka wuce.

1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.

2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.

3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.

4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.

5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.

6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa

7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.

8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.

9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.

10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.

Share.

game da Author