KYARI YA KAI KARAN ‘YAN MAJALISA: Basu yadda ayi musu gwaji da na’ura sai su rika fankama suna huhhura hanci

0

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ya kai kukan sa ga shugaban majalisar tarayya, Femi Gbajabiamila, cewa ‘yan majalisa ba su bari ayi musu gwajin cutar coronavirusa filayen jirgin saman Najeriya, sai su rika fankama suna tinkaho.

” Ministan Lafiya ya kawo min karar yadda ‘yan majalisa ke nuna iko a filayen jirgin saman kasarnan, idana aka bukkaci ayi musu gwaji. Sai su rika fankama suna huhhura hanci. ba su yadda ayi musu.

” Ina so mu sani cewa wannan gwaji dole ne ayi shi ko kai waye domin shine hanya ta farko da za abi wajen kauce wa kamuwa da cututtuka musamman a wannan lokaci.

” Ina kira gareka da ka tilasta wa wadanda suka ki yadda ayi musu gwajin cutar coronavirus da su kawo kansu ayi musu tunda wuri.

Sai dai kuma ba a tabbatar da ko wasu yan majalisa bane suka kauce wa gwajin da ya kai ga har sai da minista ya kai kuka ofishin shugaban kasa.

Zuwa ranar litini, mutane 35 suka kamu da coronavirus a Najeriya, hadda dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Sannan kuma duk a yau ne aka samu mutum na farko da ya rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar.

1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.

2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.

3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.

4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.

5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.

6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa

7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.

8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.

9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.

10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.

Share.

game da Author