BAUCHI: Cikin mutane 60 da aka yi wa gwajin coronavirus 47 basu kamu ba

0

Kwamishinan Lafiya na Jihar Bauchi Aliyu Maigoro, ya ce ba a samu cutar coronavirus a jinin mutane 47 cikin 60 da aka yi wa gwajin cutar.

Idan ba a manta ba, tun bayan tabbatar da kamuwa da cutar da aka yi wa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, aka nemi mutane musamman wadanda suka yi mu’amula da gwamnan da makarraban sa su garzayo a duba su.

An yi wa mutane 60 gwaji amma kuma sakamakon da ya fito zuwa yanzu ya nuna babu mai dauke da cutar a cikin 47 da aka dawo da su.

Kwamishina Maigoro ya ce suna sauraren sauran sakamakon gwajin da aka mika wa hukumar NCDC.

” Ya kamata a ce an dibi jinin mutane fiye da haka, sai dai kuma mun samu cikas din rashin robobin saka jini da ake diba. Ba mu da su da yawa. Haka ya sa dole a dakata tukunna.

” yanzu haka muna jiran wasu su taimaka mana da robobin ko kuma kwalaben adana jini, domin mu ci gaba da diban jinin mutane.

Sai dai kuma har yanzu ba a san ko mutane nawa bane ake so a gwada jinin su a jihar, domin akwai wadanda sun yi cudanya da wandanda suka kamu da yawa a gardagar ko kuma cudanyar wanda ya yi da wanda ya yi cudanyar.

Share.

game da Author