An samu karin mutane 11 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Adaddin masu dauke da cutar ya lula daga 70 zuwa 81.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce takwas daga cikin 11 din a jihar Legas ne, biyu daga Enugu daya kuma da jihar Edo.
Yan zu mutum 81 kenan ke dauke da cutar a Najeriya
Uku sun warke sannan daya ya mutu.
NCDC ta sanar da haka ne da misalin karfe 11:55 na daren Juma’a.
Idan ba a manta ba da misalin karfe 8:00 na yamman ranar Juma’a ne NCDC ta sanar cewa an samu karin mutane 5 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
NCDC ta ce uku a Abuja suke biyu a jihar Oyo.
A yanzu dai mutane 81 ne ke dauke da cutar , uku sun warke sannan daya ya mutu.
Lagos- 52
FCT- 14
Ogun- 3
Ekiti- 1
Oyo- 3
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-1
Rivers-1
Enugu- 2
Matakai 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.