TASHIN HANKALI: Coronavirus ta kashe mutane sama da 900 cikin awa 24 a kasar Italiya

0

A cikin awa 24 mutane sama da 900 suka mutu a kasar Italiya.

A yanzu mutane sama da 25,000 ne Suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar a duniya. Sannan kasashen Italiya, Spain, Amurka na cikin kasashen da cutar ta yi wa kamun talala.

Manana kimiya na zaton cewa da dama sun mutu a kasar Italiya ba tare da an yi gwajin ba.

Kasar Italiya irate kasa na biyu a duniya da ta fi yawan samun mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da coronavirus.

DALILIN DA YA SA MUTANE KE MUTUWA A KASAR ITALIYA

Masana kimiyya sun ce rashin gaggauta saka dokar hana walwala na daga cikin dalilan da yada cutar a kasar.

Sannan kasar na da tsofaffi da dama da ke fama da wasu cuta a jikin su shine ya sa da zaran coronavirus ya kama su sai su fada cikin halin ha’ula’i.

Adadin yawan tsofaffin dake kasar Italiya sun kai kashi 87 sannan da dama daga cikinsu sun zarce shekaru 70.

A yanzu dai kasar ta saka kafa dokar hana walwala sannan ta dakatar da duk aiyukkan kasuwanci dake tsakanin ta da kasashen Chana da Cuba.

Tunda annobar coronavirus ya game duniya, ba a samu rana daya da aka samu yawan mutane har sama da 900 ba da suka mutu kamar wadanda suka mutu ranar Juma’a a kasar Italiya.

Bayan haka an samu karin yawan mutane da suka kamu da cutar a kasar.

Share.

game da Author