Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tir da harin da mahara suka kai kauyukan jihar Katsina inda suka kashe akalla mutane 30.
Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya bayyana haka a sako daga fadar gwamnatin tarayya.
Shehu ya ce, shugaba Buhari yayi kira ga ‘yan baga dake ayyukan sa kai a kauyuka da su rika mika ‘yan ta’adda idan suka kama su ga ‘yan sanda maimakon daukan hukunci a hannun su.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya yi karin bayanin cewa wasu mahara da suka kai akalla su 100 sun afkawa kauyukan Damkal da Tsanwa duk dake karamar Hukumar Malumfashi inda suka kashe mutane akalla 30.
Gambo ya ce maharan sun afkawa wadannan kauyuka biyu ne da misalin karfe biyun dare sannan suka rika cinna wa gidaje, rumbunan hatsi da dabbobi wuta.
Bayan haka sun rika bude wuta ta ko ina da bindigogi.
Rahoton kakakin ‘yan sandan ya nuna cewa yara kanana ne da tsoffi aka fi kashe wa da yake ba za su iya arcewa a lokacin da maharan suka afka musu ba.
Jihar Katsina kamar sauran jihohin yankin Arewa na ciki tsaka mai wuya game da hare-haren ‘yan ta’adda da yaki co yaki cinyewa.
Da yawa daga cikin mazauna wasu kauyukan jihar tuni sun yi hijira zuwa garuruwan da suka yi iyaka da musamman jihohin Kaduna, Kano, Sokoto da dai sauransu.