A ranar Laraba ne kotun majistare dake Abeokuta jihar Ogun ta yanke hukuncin daure wani magidanci mai shekaru 37 mai suna Mutiu Sonola a kurkuku bayan ta kama shi da laifin kashe matarsa da tsananin duka.
Alkalin kotun Olakunleyin Oke ya yi watsi da rokon sassauci da Sonola ya nema sannan ya yanke hukuncin daure shi a kurkuku har sai an kammala yin shawara da hukumar gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Dan sandan da ya shigar da karar Olubalogun Lawrence, ya bayyana cewa Sonola ya aikata wannan mummunar aiki ne ranar 25 ga watan Disemba da misalin karfe 2 na rana a gidansu dake Ijeun Tutun a Abeokuta.
Lawrence ya ce a wannan rana matar Sonola wato Zanain Sotayo mai shekaru 34 ta nemi izinin mijinta domin ta je gidan oganta domin shagalin bukin kirsimati inda shi Sonola ya hana.
” Bayan ta tambayeshi, shi kuma Sonola ya hana sai suka kaure da musu har ya kai ga dambe. A haka ne dai garin kokuwa sai ya doke kanta a bango. Daga nan sai aka garzaya da ita asibiti inda bayan likita ya duba ta sai ya ce ai ta cika.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 2 ga watan Afrilun 2020.