Kungiyar Bin Dididdigin Sahihancin da Nagartar Ayyuka ta SERAP, ta kalubalanci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fito ta yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe bilyoyin dalolin da aka rika karbowa daga kasashen da aka rika amso kudaden da sace aka kai a aka boye a zamanin gwamnatin marigayi Sani Abacha.
SERAP ta aika wa da wasikar neman a yi wannan bayani ga Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, Ministan Shari’a, Abubakar Malami da kuma Babban Akanta na Tarayya.
A cikin wasikar wadda Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu ya aika a ranar 14 Ga Fabrairu, 2020, ya nemi a fito a yi wadannan bayanai da ke kasa a cikin mako daya, wato kwanaki bakwai.
Bukatun Da Ke Nema Daga Gwamnati
SERAP na so a bayyana adadin ayyukan da aka yi da makudan kudaden satar da aka karbo na Abacha, daga kasashen waje tun daga 1999 zuwa yau.
Ta nemi a bayyana kwangilolin dalla-dalla ko guda nawa ne da kuma wurraren da aka yi su.
Ta nemi a bayyana adadin yawan kudaden da kowace gwamnati ta karbo daga waje na kudaden Abacha, tun daga 1999 zuwa yau.
Ta na bukatar a bayyana sunayen kamfanonin da aka bai wa kowace kwangila da kuma adadin yadda aka bayar da kwangilar.
Ta na so a fadi ko wane birni, jiha, lungu ko sako aka yi kwangilar.
SREP ta ce wajibin kowane dan Najeriya ne ya san yadda aka rika kashe kudaden.
Ta ce daga 1999 zuwa yau, an maido wa Najeriya dala bilyan 5 daga kudaden Abacha, amma har yau babu wani sahihin aiki ko ayyukan da za a iya nunawa a ce an yi da kudaden.
SERAP ta yi zargin cewa akwai alamomin an yi sata-ta-saci-sata da makudan kudaden, ko kuma an yi almubazzaranci da su.
SERAP ta ce gwamnati ce ta bayar da kofa ake tantama, waswasi da kokanton yadda aka yi da kudaden, domin ba ta fitowa ta na yi wa ‘yan Najeriya cikakken jawabin abin da aka yi da kudaden.
Ta ce dokar bayyana bayanan gwamnati, wato FoI, ta wajabta wa gwamnati bayyana yadda ta ke kashe kudade. Kuma ta hana kumbiya-kumbiya. Don haka ta na so a bayyana wadannan bukatu da ta nema a cikin kwanaki bakwai bayan aikawa da wasikun ta.
SERAP ta ce idan ba a yi haka ba, za ta dauki mataki na gaba, kuma ‘yan Najeriya za su rika tababa da kokwanton sahihancin yaki da cin hanci da rashawa, wanda gwamnatin Buhari ke tinkahon cewa ta na yi.
Idan gwamnati ta bayyana yadda aka yi da kudaden kuwa, to SERAP ta ce kwarjinin ta zai karu a idon jama’a a cikin kasar nan da ma duniya baki daya.