Sai Buhari ya ga dama zai bayyana kadarorin sa – Fadar Shugaba

0

Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wata dokar da ta tilasta wa shugaban kasa cewa lallai-lallai sai ya bayyana kadarorin sa.

Fadar Shugaban Kasa ta yi wannan raddi ne ga Kungiyar SERAP, wadda ta bai wa Shugaba Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo su bayyana kadarorin su a cikin kwanki bakwai.

Cikin wata sanarwa da SERAP ta fitar ranar Lahadi, ta ce rashin bayyana kadarori da Buhari da Osinbajo suka yi, “ya gurgunta nagarta nauyin da tsarin mulki ya wajabta na bayyana kadarori.”

Sai dai kuma kakakin Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa babu wata doka da ta tilasta wa Buhari bayyana kadarorin sa a zangon sa na biyu.

Ya ce bayyana kadarorin sa a wannan lokacin ba tilas ba ne, sai idan ya ga dama kawai.

“Shugaban Kasa zai yi dukkan abin da doka ta wajabta masa yi, kuma zan iya cewa shi dai shugaban kasa ya rigaya ya bayyana kadarorin sa.

“Bayyana ta a fili ba ya cikin dokar Najeriya, amma ganin dama ce kawai.” Inji Adesina.

PREMIUM TIMES ta tunatar da cewa Buhari da Osinbajo sun bayyana wasu kadarorin su a farkon zangon su na farko, 2015.

Dokar bayyana bayanai na ma’aikacin gwamnati, ya bai wa kowane dan Najeriya damar ya nema kuma a bayyana masa dukkan bayanan da ya ke nema na wata hukumar gwamnati ko cibiya ko ma’aikata, banda bayanan tsaro kadai.

Adesina ya ce dukkan bayanan kadarorin Buhari da na Osinbajo na hannun Hukumar CCB, kuma za ta iya bayyana su idan ta ga dama.

A daya duk wani kokari da aka yi domin CCB ta bayyana kadarorin ya ci tura, domin ta ce doka ba ta ba ta umarni ko iznin bayyanawa ba.

Share.

game da Author