Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da ikon ya tirsasa ko bada shawarar a kara kudin wutar lantarki ko a rage.
Kakakin Yada Labarai, Femi Adesina ne ya yi wannan bayani, a cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talbijin na Channels, a jiya Litinin, inda ya ce batun karin kudin wutar lantarki, magana ce daga Ma’aikatar Inganta Makamashi da Hukumar NERC, wadda ke da hakkin kara kudin wuta da kayyade shi, ba daga tunanin Buhari ba.
Ranar Lahadi ne PREMIUM TIMES ta buga rahoton yadda hukumar NERC ta bayyana karin kudin wuta ga kamfanonin saida wutar lantarki 11 na kasar nan, wato DisCos.
Wannan karin kudi da aka yi ya haifar da guna-guni ga jama’a masu nuna rashin jin dadin yadda aka yi karin, musamman karya kumallon da suke korafi cewa an yi da karin a farkon shiga shekarar 2020.
Amma Adesina ya bayyana cewa wannan tunani ko shawarar karin kudin wuta ba daga Buhari ya fito ba.
“Wannan batun karin kudin wuta ba aikin Shugaban Kasa ba ne, amma batu ne daga hukumar da abin ya shafa, wato Ma’aikatar Inganta Makamashi, sai kuma Hukumar Kayyade Kudaden Lantarki, wato NERC.
“Amma kuma a yanzu ita NERC din ta bayyana cewa karin ba zai fara amfani ba ko fara amfani da shi har sai farkon watan Afrilu.”
Daga nan sai ya kara da cewa ya yi kusa sosai wai a ce Buhari ya shiga maganar tun a yanzu.
A karshe ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da cewa an yi abin da jama’a ke so a duk wani al’amari da gwamnati za ta gudanar.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda aiki Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a ranar 1 Ga Janairu, 2020, shi ne karin kudin wutar lantarki har zuwa kashi 78% bisa 100% daga yadda ake shan wutar tun daga 2015.
Daga 1 Ga Janairu, 2020 za a fara shan wutar lantarki a sabon farashin da ba na 2015 ba, kamar yadda Hukumar Kayyade Farashi da Adadin Wutar Lantarki ta Kasa, NERC ta fitar da sanarwa.
NERC ta fitar da wannan sanarwa ce ga dukkan Kamfanonin Saida Wutar Lantarki 11, wato Discos a ranar 31 Disamba, 2019. Amma dai sai ranar Asabar ce NERC din wallafa labarin karin farashin a shafin ta.
Shugaban Hukumar NERC, Joseph Momoh da Shugaban Kula da Lasisin Kamfanonin Saida Lantarki, mai suna Defe Akpanye ne suka sa wa sanarwar hannu, wadda tuni aka raba wa Discos 11 ita.
Wannan sanarwa na dauke da bayani dalla-dalla na karin kudin da kowane mai shan wutar lantarki zai rika biya daga ranar 1 Ga Janairu, 2020 kenan.
Misali, an yi karin kashi 57% bisa 100% na farashin lantarki a Ikeja, Lagos, yayin da a Enugu kuma aka yi karin kashi 77.6.
Mazauna Enugu na biyan naira 13.4 ga kowane ‘yunit’ na wuta kWh tun daga 2015. Amma daga 1 Ga Janairu, 2020 za a rika cajin su naira 21.8 kowane ‘yunit’.
A Enugu kuma tun daga 2015 su na shan ‘yuni’ din lantarki duk guda daya a kan naira 17.44. Amma daga yanzu za a rika cajin su naira 30.93.
Masu amfani da wutar lantarki a gidaje kuwa, an yi wa karin masu gidajen da aka kebe a matsayin Rukunin R2 da R3, a yanzu za su rika biyan naira 21.30 da kuma 21.80. A baya kuwa su na biyan naira 13.34 da kuma naira 26.5.
Kamfanonin Saida Wutar Lantarkin da aka tura wa wannan sanarwa sun hada da Abuja Electricity Distribution Company, sai na Kaduna, Kano, Ikeja, Jos, Enugu, Eko, Ibadan, Fatakwal, Yola da na Benin.
Rukunin Gidajen da ke shan wuta a kan naira 27.20 a Abuja, yanzu za su rika biyan naira 47.09.
Karin kudin wutar ya zama ruwan dare game-duniya, domin ya shafi masu gidajen zama, masu kananan sana’o’in hannu, masu masana’antu, gidan ruwa, masu sarrafa kayayyaki da sauran su.
Rukunin Gine-ginen Kasuwanci da ke biyan naira 20.45 kowane ‘yunit’ tun daga 2015, a yanzu an yi musu kari, za su rika shan kowane ‘yunit’ a kan naira 37.39.
Su kuma Rukunin da ke shan lantarki a naira 27.20, yanzu sai sun rika biyan naira 47.09 a kowane ‘yunit’.
Dalilan Karin Kudin Lantarki
Kadan daga dalilan karin kudin lantarki da Hukumar NERC ta bayar na karin kudin wutq, sun hada da karin farashin kayayyaki da ya haifar da kudade masu yawa ke sayen kaya kalilan, zuwa karin kashi 11.3 daga Janairu 2019 zuwa Oktoba 2019.
Sai kuwa yadda farashin dala daya da gwamnati ta kayyade a kan naira 306, amma sai jidalin naira 3 hau kan ta, zuwa 309, sai kuma yadda farashin man gas ya kai dala 2.50 a kowace ‘metric tons’ milyan daya.
A karshe Hukumar NERC ta gargadi Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Kasa, TCN cewa shi za a kama da laifi idan wani kamfanin Saida Lantarki ya ki bin wannan umarni na karin kudin wutar lantarki.
Amma cikin wata sabuwar sanarwa da NERC ta fitar jiya Litinin, ga dukkan Kamfanonin Saida Wutar Lantarki 11, wato Discos, ta ce sai daga ranar 1 Afrilu, 2020 za a fara amfani da sabon farashin da ta kayyade ko kuma a ce ta kara.