BAUCHI: UNICEF za ta raba maganin Kanjamau kyauta wa mata masu ciki

0

Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta ce za ta raba maganin cutar kanjamau wa mata masu ciki a jihar Bauchi.

UNICEF ta ce za a raba wadannan magungunan ne a duka cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 323 dake jihar.

Asusun ta kuma ce ta yi wannan tanadi ne ganin cewa wadannan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar na kula da mata masu ciki kyauta.

Shugaban asusun a Najeriya reshen jihar Bauchi Bhanu Pathak yace UNICEF ta yi haka ne domin kawo karshen yadda mata ke yawaita haihuwar jarirai dauke da cutar.

Idan ba a manta ba sakamakon binciken da hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) gabatar ya nuna cewa a Najeriya mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar sannan masu shekaru kasa da shekara 64 ne suka fi yawa.

Binciken ya nuna cewa daga cikin jarirai 160,000 masu dauke da cutar da ake haifowa a duniya 37,000 daga Najeriya suke.

Share.

game da Author