Mun shirya gudanar da zabukan-cike-gurbi ranar Asabar – Hukumar Zabe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan cike-gurbi a wurare 28 cikin jihohi 11 na kasar nan.

Daga nan sai INEC ta yi gargadin cewa ba za ta amince da sauya dan takara, domin lokacin canja dan katara ya wuce.

INEC ta bayyana ranar shirya zabukan ne a fadin kasar nan, wadanda za ta gudanar bayan da hukunce-hukunce 30 da kotuna daban-daban suka zartas cewa a sake zabukan a wuraren da hukunce-hukuncen suka shafa bayan kammala zabukan 2019.

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya bayyana haka a ranar Talata, a lokacin da ya ke rantsar da wasu sabbin Shugabannin Zabe, wato Kwamishinonin INEC ta Tarayya.

An yi kwarya-kwaryan bikin rantsar da su a hedikwatar INEC a Abuja.

A lokacin ne Yakubu ya bayyana cewa, “shida dga cikin zabukan cike gurabun 28 za a yi su ne ga ilahirin mazabun da abin ya shafa.

“Yayin da kuma 22 daga cikin su za a yi ne a wasu daidaikun mazabu.”

“Wuraren da kawai INEC za ta iya amincewa da sauya dan takara sun hada da: Dan takarar Majalisar Tarayya na Karamar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi, Dan Majalisar Jiha na Karamar Hukumar Agwara cikin Jihar Neja, inda za a gudanar da zabuka babu yan takarar da aka rigaya aka bayyana su ne suka yi nasara da farkon gudanar da zaben a cikin 2019.”

Daga nan sai shugaban na INEC ya kara tabbatar wa ’yan Najeriya cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe.

Ya ce hukumar zabe za ta yi aiki kafada-da-kafada da jami’an tsaro, masu sa-ido da kuma ’yan jarida.

Ya ce INEC ta shirya tsaf wajen kai kayan zabe da wuri da kuma fara zabe da wuri, har ma da isar jami’an zabe da wuri.

Share.

game da Author