Trump zai hana ‘yan Najeriya shiga Amurka

0

Kafin karshen wannan wata na Janairu ne Shugaban Amurka Donald Trump, zai kakaba wa ‘yan Najeriya dabaibayin karakaina zuwa Amurka.

Wata sanarwa da jaridar Wall Street Journal ta Afrika ta buga, ta tabbatar da cewa za a kakaba takunkumin ne kan Najeriya da wasu kasashe shida.

Kasashen bakwai da wannan doka za ta shafa sun hada da Najeriya, Belarus, Eritrea, Kyrgyzstan, Myanmar, Tanzania da kuma Sudan.

Trump ya tabbatar da shirin sa wannan takunkumi a ranar Talata a Davos, cewa gwamnatin sa ba da dadewa ba zai kakaba wannan takunkumi, wanda idan an fara amfani da shi, zai yi wahala ‘yan Najeriya da sauran ‘yan sauran kasashen shida su iya samun biza zuwa Amurka.

Takunkumin da Trump zai kakaba wa kasashen bakwai zai danganta daga wannan kasa zuwa waccan, bisa la’akari da dalilan da Amurka za ta bayar na kakaba wa kowace kasa na ta takunkumin.

An dai yi hasashen cewa takunkumin zai dogara ne kan dalilai na tattalin arziki da kuma na tsaro.

Wannan sabon tsari dai ci gaba ne daga adadin wasu kasashe da Trump ya fara sa wa takunkumin hana su shiga kasar sa, cikin 2017 lokacin da bai dade da hawa mulki ba.

Kasashen Venezuela, Somalia, Yemen, Libya da Koriya ta Arewa ne Trump ya kakaba wa dokar hana shiga Amurka a farkon hawan sa.

Wannan takunkumi da Trump ya kakaba dai wasu ba ji dadin sa ba a cikin Amurka.

Hakan ta sa sun garzaya kotu suka yi nasara a kan Trump. Sai dai kuma da Trump ya garzaya Kotun Koli, ya yi nasara a kan wadanda suka kai kara.

Kasar Chadi na daga cikin wadanda Trump ya hana shiga Amurka cikin 2017, amma an cire sunan ta daga baya a cikin 2019.

An cire sunan Chadi bayan da jami’an Amurka suka bayyana wa Trump cewa ta cika sharuddan da Amurka ta gindaya.

Kamfin din Trump na takaita shiga ko kwararar bakin-haure cikin Amurka ya yi kamari tun a farkon hawan sa mulki.

Ta kai har ya gina Katanga tsakanin kan iyakar kasar da Mexico, a yankin da bakin-haure ’yan Mexico ke kwarara cikin Amurka.

Idan ba a manta ba, cikin 2017 Trump ya nuna damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke makalewa idan sun je Amurka, ba su komawa gida.

Wannan ta kai ga yi wa ’yan Najeriya gori, ya na cewa, “idan ‘yan Najeriya sun shigo Amurka, ba su son komawa cikin bukkokin su.”

Haka dai jaridar New York Times ta Amurka ta buga, kuma har yau Najeriya ba ta maida ma ta martani ko raddi ba.

Share.

game da Author