Daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha mallakin jihar Kaduna, Nuhu Bamalli Polytechnic, sun tattare kofofin shiga wannan makaranta tun da safiyar Alhamis.
Daliban sun ce suna zanga-zanga ne domin jawo kan hankalin mahukuntar makarantar da gwamnatin jihar Kaduna game da rashin wutan lantarki da suke fama dashi da matsanancin rashin tsaro a makaranta.
Daliban sun fito babban titin dake zagaye da makarantar dauke da kwalaye sannan suka garkame kofofin shiga.
Discussion about this post