Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta kara yawan wuraren yin gwajin wasu manyan cututtuka a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka a Abuja.
Ihekweazu ya ce an bude wadannan wurare ne a babbar asibitin koyarwa na jami’ar Benin dake jihar Edo (UBTH), asibitin koyarwa na jami’ar Enugu (UNTH) da ofishin hukumar NCDC dake babban birin tarayya Abuja.
Ya ce wadannan wuraren za su fi maida hankali ne wajen gwajin cututtukan bakon dauro, shawara da Rubella.
“ NCDC ta gina wadannan wuraren sannan asibitocin da aka gina wuraren yin gwajin za su dauki nauyin samar da ma’aikata, kayan aiki da tabbatar da cewa wurin na aiki yadda ya kamata.
Ihekweazu yace NCDC ta mai da hankali wajen ganin an samar da wuraren gwajin cututtukan bakon dauro da shawara saboda cututtukan na daga cikin wadanda suka yi wa kasa Najeriya katutu har yanzu.
“ A shekarar 2019 wuraren yin gwajin cututtukar bakon dauro, shawara da Rubella guda hudu ne kawai sannan babu ko daya a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
“Hakan da muka yi zai taimaka wajen dakile yaduwar cututtukar musamman a wuraren dake fama da matsalar rashin wurin yin gwaji.
A karshe Ihekweazu ya bayyana cewa NCDC ta gina wadannan wurare ne da tallafin da ta samu daga kungiyoyin bada tallafi da suka hada da GAVI, hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka, Gidauniyyar ‘Resolve to save lives’, kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da sauran su.