kungiyar samar da tallafi mai suna ‘RBM Partnership to End Malaria’ ta bayyana cewa ta raba gidajen sauro akalla biliyan biyu a kasashen duniya.
Kungiyar ta ce ta fara rabon gidajen Sauron ne tun a shekarar 2004 wanda hakan ya taimaka wajen kawar da zazzabin cizon sauro da kashi 68 bisa 100 a kasashen Afrika.
Tsakanin shekarar 2010 zuwa 2018 adadin yawan mata da yara kanana da suke amfana da gidajen sauro a wannan yanki ya karu daga kashi 26 zuwa kashi 61 bisa 100.
Daga nan an kuma samu sauki wajen farashin gidajen sauro a kasuwannin duniya domin daga shekarun 2006 zuwa 2017 farashin gidajen sauro ya ragu daga dala 4.50 zuwa dala 2.
Shugaban kungiyar Abdourahgmane Diallo ya kara da cewa an samu nasarar rage yaduwar wannan cuta ne a dalilin hada hannun da kungiyoyin bada tallafi suka yi sannan ta kokarin da gwamnatin kasashen duniya ke yi.
“ Hakan zai yiwu ne idan dukan sassan gwamnati da duk fannoni sun hada hannu wajen ganin bayan wannan cuta.