Yadda ‘yan uwan mai jinya suka yi wa malamar Asibiti zindir saboda kin bin umarnin su

0

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa baza ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta kwato wa ma’aikatan kiwon lafiya hakkunan su ko da zai kai ga a shiga kotu ne.

Shugaban kungiyar rashen babban birnin tarayya Abuja Ekpe Phillips ya fadi haka ne a cikin wannan mako a dalilin tozarta wata likita da wasu ‘yan uwan wani mara lafiya suka yi a asibitin Maitama.

Phillips ya ce ‘yan uwan wannan mara lafiyan sun lakadawa likitan duka sannan suka yi mata zindir a cikin mutane saboda likitan ta ki yin abin da suke so ta yi musu.

” Wani mara lafiya ne aka kawo asibitin. Da likatar ta duba shi sai taga ya na bukatar kula matu, daga nan sai ta rika ririta shi ta yi kokarin bashi dukkan kulan da yake bukata. Daga baya sai ‘yan uwan mai jinyar suka shawarci likitar da akara masa jini.

“Likitar ta ce dasu a bisa binciken ta mara lafiyar ba jini yake bukata ba. Duk abin da yake bukata ta yi mishi yanzu. Daya ke ba mai tsawon kwana bane sai daga baya Allah yayi masa rasuwa.

” Aiko da ga rasuwar sa sai wadannan ‘yan uwan marigayin suka hau surfar wannan likita cewa jini da ta ki kara masa ne yasa ya riga mu gidan gaskiya. Dukan yayi tsanani da har tsirara suka yi mata a asibitin.

Daga nan sai ya kira ga mutane cewa su daina daukar doka a hannun su. Idan aka yi musu laifi su rika danne zuciyar su su kai kara gaba. Ba su hau dukar likita ba.

Ya kara da cewa ba za su zuba ido ba a rika ci wa ma’aikatan su mutunci haka kawai daga yanzu.

Share.

game da Author