BUHARI YAYI MURABUS: ‘Idan mai fada wawa ne, mai saurare ba wawa bane’ – Fadar Shugaban kasa

0

Fadar shugaban kasa ta maida wa sanata Abaribe martani na kira da yayi wai shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus saboda matsalar tsaro da yaki ci yaki cinyewa a kasar nan.

Abaribe da wasu sanatoci sun soki salon mulkin gwamnatin Buhari musamman a wajen harkar samar da tsaro a kasa Najeriya.

Abaribe ya yi kira ga shugaba Buhari ya yi murabus tunda ya kasa tabuka abin azo a gani a harkar tsaron kasar nan.

” ‘Yan Najeriya sun zabi APC da Buhari ne domin yayi alkawarin samar musu da tsaro. Tunda abin ya gagara sai ya tattara ya yi murabus kawai.” Inji Abaribe.

Fadar shugaban kasa ta ce wannan batu bata mai hankali bace domin idan har Buhari zai yi murabus toh ashe miliyoyin ‘yan Najeriya ma za su yi murabus harda shi kan sa Abaribe din.

” Idan fa ba a manta ba Abaribe ne ya tsaya wa dan taratsin nan Nnamdi Kanu sannan shine yayi sanadiyyar waskewarsa da har yanzu ba a san inda yake ba.

” Ya kamata a ce tunda shine ma ya tsaya masa kuma gashi bai dawo ba a tasa keyarsa.

Garba Shehu da ya fitar da sakon fadar shugaban kasan ya kara da cewa shugaba Buhari na kokarin gaske wajen ganin kasa Najeriya ta zauna lafiya sannan an samu tsaro a ko-ina a fadin kasar.

Baya ga kira da wasu suka yi da shugaba Bubari ya yi murabus wasu sanatocin sun nemi da a tumbuke duk shugabannin rudunar tsaron kasar nan cewa kwakwalwar su ta dode ba su da wasu sabbin dabaru da za su iya amfani da wajen kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Share.

game da Author