Najeriya za ta kara karbo dala milyan 321 da Abacha ya kimshe kasar waje

0

Gwamnatin Najeriya ya bayyana cewa za ta dawo da karin dala milyan 321 da tsohon Shugaban Kana na mulkin soja, Sani Abacha ya sata ya kimshe kasashen waje.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya bayyana haka, sannan kuma ya kara da cewa nan gaba kadan za a kwace wasu kadarori na James Ibori da na tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Allison Diezani-Madueke.

A ranar Laraba ne Minista Malami ya bayyana wa manema labarai haka, bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaba Muhammadu Buhari.

Ana sa ran cewa cikin mako mai zuwa ne za a rattaba hannun yarjejeniyar dawo da kudin da Abacha ya boye a kasar waje, kamar yadda Malami ya bayyana.

Malami ya ce Najeriya da Amurka da Tsibirin Island of Jersey ne za su rattaba yarjejeniyar.

Ministan ya ce idan an karbo kudin za a zuba su ne wajen ci gaba da ayyukan raya kasa da suka hada da aikin babban titin Lagos zuwa Ibadan, Abuja zuwa Kano da kuma Gadar Kogin Neja da ake kan aikin ginawa.

Wasu Kudaden Sata

Malami ya kara da cewa akwai kuma wasu dala milyan 6.8 da tsohon Gwamnan Delta, James Ibori ya sata wadanda za a maido.

“A yanzu haka mun kammala zaman amincewa a dawo za dala milyan 321 da Abacha ya sace, har ma da wasu kudi da James Ibori shi ma ya wawura.” Cewar Malami.

Idan ba a manta ba, cikin 2016 dai Shugaba Buhari ya taba furta cewa, “ Abacha ba barawo ba ne.” Duk kuwa da cewa ga kudaden da ya wawura ana dawo da su Najeriya.

Duk da irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya ke ikirarin Diezani ta sata, har yau an kasa dawo da ita Najeriya domin ta amsa tuhuma.

Share.

game da Author