Shugaban kungiyar manoman Timatir na kasa Sani Danladi-Yadakwari,ya koka kan yadda manoma ke fama da karancin Irin Timatir na zamani ganin cewa lokacin noman sa ya kusa wucewa.
Yadakwari ya bayyana haka ne da yake hira da kamfanin dillancin Najeriya a Kano ranar Talata.
” Babban Bankin Najeriya ta ba kamfanin Dangote naira biliyan 1.58 domin samar wa manoman timatir irin timatir na zamani daga kasashen waje. Amma a halin yanzu da muke hira da kuku mutane 452 ne kawai suka samu wannan iri cikin manona 10,000 da suka yi rajista da mu.
” Abin da ke tada mana hankali shine idan har ace zuwa yanzu ba a iya samar wa manoma wannan iri ba, to fa lallai akwai yiwuwar ayi fama da karancin timatir a cikin shekara mai zuwa.
” Shi timatir akan noma shi ne a lokacin rani. Zuwa tsakiyar watan janairun 2020 idan ba a iya samar wa manoma da dama irin ba to shikenan sai dai kuwa wata shekarar domin daga lokacin ba zai yiwu a noma timatir din ba.
Yadakwari ya ce ya kamata ace zuwa yanzu an rabawa akalla koda rabi ne daga cikin manoman da suka yi rajista da kungiyar amma ace wai manoma dari hudu da ‘yan kai ne suka iya samun wannan iri.
” Ina kira ga Kamfanin Dangote da aka ba kwangilar shigo da wannan iri da su gaggauta samar wa manoma irin domin fa an kashe kudi wajen gyaran gona domin wannan aiki.
Da ya ke karin bayani game da matsalolin da aka sami wajen samar da irin shugaban Kamfanin Gonakin Dangote, Abdulkarim Kaita ya bayyana cewa sun dan samu matsala ne da babban bankin kasa wajen samar musu da kudaden sannan kuma ko a wajen shigo da irin sai an dauki lokaci wajen wanyewa da jami’an hukumar shige da fice ta kasa.