Bayanai da suka iske mu sun nuna cewa hukumar tsaro ta SSS na shirin sakin tsohon maiba shugaban kasa shawara kan harkokin Tsaro, Sambo Dasuki a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da mawallafin jaridar Sahara Reporters da duk ke tsare.
Hukumar ta gayyaci lauyoyin Dasuki da Sowore su garzayo ofishinta maza-maza domin cika takardun sakin su.
Tuni dai Lauyoyin suka gaggauta garzaya ofishin hukumar dake Asokoro domin amsa wannan gayyata.
Hukumar SSS ta tsare Dasuki tun a watan Disambar 2015 a bisa zargin harkallar dala biliyan 2 kudin makamai a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.