Yayin da milyoyin mazauna sansanonin masu gudun hijira, da ma wadanda suka tsere kasashe makwauta ke fama da matsananciyar yunwa, su kuma ma’aikatan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA sun shiga watandar kayan abincin da ake warewa domin raba wa mazauna sansanin gudun hijira.
Majalisar Dinkin Duniya dai a cikin Agusta ta bayyana cewa kimanin mazauna yankin Tafkin Chadi milyan 3.6 ne ke fama da matsananciyar yunwa da rashin abinci.
Baya ga wadannan kuma akwai dubun dubata wadanda suka fada cikin kunci sakamakon hare-haren Fulani makiyaya.
Sai dai duk wannan mawuyacin hali da jama’a ke ciki, hakan bai hana ma’aikatan NEMA cire tausayi a zukatan sub a, suka rika kwasar abincin da ya kamata a bai wa masu gudun hijira su na rabawa a jajibirin Kirsimeti.
Wani ma’aikacin NEMA da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa kusan duk jihohin kasar nan, babu inda ofishin NEMA bai raba kaya a wannan lokaci na Kirsimeti ba, kuma kayan abincin da ya kamata a raba wa masu gudun hijira ne.
“Ana raba kayan abincin ga dukkan ma’aikatan NEMA a fadin kasar nan.” Haka ya shaida wa wakilin mu.
Wakilinmu ya gani da idon sa a El-Rufai Plaza, Wuse Market, Abuja, yadda aka rika raba kayan abincin na masu gudun hijira ga su ma’aikatan NEMA din.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa wata babbar ma’aikaciyar NEMA ce mai suna Chinwe Okpara aka dora wa nauyin tsara raba kayayyakin abincin wanda hakkin masu gudun hijira ne.
Chinwe ta rika kiran ma’aikata cewa kowa ya garzayo ya yi sauri ya karbi kason sa, idan kuma ya yi latti, to za a bai wa wani mai rabo.
Motoci kirar Hilux kimanin goma da aka rika loda wa kayan abinci daya bayan daya, ciki har da wata mai lamba “O2R-82FG”.
An ci gaba da watandar kayan abinci har ranar Litinin, wannan karo a ofishin NEMA da ke kan Titin Mombolo, Wuse Zone 2, Abuja.
PREMIUM TIMES ta lura cewa an rika watandar kayan abinci a ofishin NEMA na Wuse Zone 2, tun daga 12 na rana har zuwa 4:30 na yamma.
Wakilin mu ya je wurin da ake watandar kayan amma a matsayin wanda ya je wucewa, ya ke tambayar abin da ke faruwa.
Ya tambayi wani ma’aikacin NEMA mai suna Isa Andrew da ke watandar kayan abinci, ya tambaye shi ko gwanjon kayan abinci ake yi, sai Andrew ya ce masa a’a.
“Ba gwanjo ake yi ba. Ana raba wa ma’aikatan mu ne ihisanin karshen shekara.” Haka ya amsa tambayar da aka yi masa, ba tare da sanin cewa wakilin PREMIUM TIMES ne ya yi masa tambayar ba.
An raba wa manyan ma’aikata babban buhun shinkafa, man girki lita 25, babban buhun sukari, katan din tumatir din gwangwani da kuma taliya. Haka aka bai wa kowanen su.
An raba wa kananan ma’aikata katan din tumatir din gwangwani kari, karamin buhun shinkafa, kwalin Maggi biyu kowane, da man girki, da sauran su.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na NEMA, Manzo Ezekiel ya karyata wannan rahoto, duk kuwa da cewa PREMIUM TIMES ta dauki hotuna da bidiyon lokacin da ake watandar kayan abincin.
Da PREMIUM TIMES ta ce masa ai har ta mallaki bidiyon yadda aka rika yin watandar kayan abincin da kuma hotunan, sai Manzo y ace ai PREMIUM TIMES za ta iya shirya bidiyon da kan ta, don ta bata sunan ma’aikatan NEMA.