A wannan raddi karo na biyu da Fadar Shugaban Kasa ta maida wa jaridar PUNCH, ta zargi jaridar da taya-bera-bari tare da haddasa rudu.
Sai dai kuma rahoton martanin da Femi Adesina ya maida wa PUNCH da safiyar yau Laraba, ya nuna kamar Fadar Shugaban Kasa ba ta damu da canja wa Buhari sunan da PUNCH ta yi ba.
Amma sa’o’i bayan martanin Adesina, sai daya Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya sake sakin wani dogo kuma zazzafan martani ga PUNCH.
“Irin yadda jaridar PUNCH ta bayyana kuma ta fassara Shugaba Muhammadu Buhari, ya nuna ta na da nifaka da kiyayya ga Shugaba Buhari. Don haka kada wannan nifaka da kiyayya ta rufe mata idanu wajen yi masa alkalancin mai adalcin da ya dace.
Shehu ya ce abin mamaki ne da kuma al’ajabi da har PUNCH ta cimma wannan makauniyar matsaya ta rika kiran Shugaba Buhari mai mulkin kama-karya, kuma Manjo Janar, wato sunan sa a lokacin da ya ke mulkin soja.
Ya ce amma yanzu Buhari ai ya yi ritaya, kuma ya zama shugaban kasa na mulkin dimokradiyya, wanda aka zabe shi har sau biyu a jere.
Ya ce wannan kadai ya nuna Buhari dan dimokradiyya ne a yanzu, ba dan kama-karya ba.
Daga nan sai ya ce wannan suna da suke neman su sauya masa, ihun-ka-banza ne, domin ‘yan Najeriya ba za su biye su ba, kuma ba za su amince da wannan sabon suna da jaridar ta ce za ta rika kiran sa ba.
Shi ma Garba Shehu, kamar yadda Femi Adesina ya fadi, ya ce bayanin da PUNCH ta buga a yau ai ya kara tabbatar da cewa akwai ‘yancin fadin albarkacin baki a karkashin gwamnatin Buhari kenan.
“A wasu kasashen duniya da babu wannan ‘yancin fadin albarkacin baki, ai ba za su iya buga irin abin da jaridar ta buga akan shugaban kasa a yau ba.”
Ya ce amma a Najeriya dan kasa na da ‘yancin buga ra’ayin da ci karo da ra’ayin gwamnati, ko kuma wannan ya yi daidai da na gwamnati.
“Amma kiran a fito a yi amfani da makami a hambare gwamnatin da jama’a suka zaba, abu ne daban wannan. Kumai ta PUNCH duk da kasassabar da ta yi a yau, ba ta yarda ta wuce gona-da-iri ta furta wannan kalamin ba. Amma ai wadanda jaridar ke kokarin karewa su sun furta wannan kasassabar.
Garba ya yi kira ga PUNCH ta ci gaba da sukar gwamnatin Buhari, amma ta rika sara ta na duban bakin gatari. Wannan shi ne cikamakin nagartacciyar dimokradiyya.
Sai dai kuma ya ce wata jarida ba ta da ikon sauya wa shugaban da aka zaba a dimokradiyance suna.
“Domin PUNCH ba ta taba canja wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo suna ba, duk kuwa da kin bin umarnin Kotun Koli ya yi, ya ki sakar wa gwamnatin jihar Lagos kudin ta naira bilyan 30, a lokacin mulkin sa.
“Sannan kuma lokacin da shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida ya sauya sunan sa zuwa shugaban kasa, PUNCH ba su yi masa bore sun ci gaba da kiran sa shugaban mulkin soja ba.
“Kai sai ma da kai Babangida ya rufe wasu kafafen yada labarai tsawon shekar, ciki kuwa har da PUNCH.
Garba ya ci gaba da buga misalai dama a matsayin raddi ga jaridar PUNCH.