Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa bashin dala bilyan 22.7 da ta shirya ciwowa za a kashe su ne waje gina ayyukan raya kasa, tattalin arziki, ba wai tasa su gaba za a yi a barbada musu gishiri da magi a lamushe ba.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed da kuma Karamar Ministar Harkokin Sufuri, Gbemisola Saraki ne suka bayyana haka.
Ministocin uku sun yi wannan bayani ne a gaban kwamitin hada-ka na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, a jiya Talata.
Kwamitocin sun hada da na Agaji, Ramce da Basussuka da na Harkokin Kasuwanci.
Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa, DMO ta bayyana a ranar 30 Ga Yuni cewa ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 25.7
Idan ba a manta ba, tun a zamanin shugabancin Bukola Saraki ne a Majalisar Dattawa Zango na 8, gwamnatin Shugaba Buhari ta bijiro musu da batun bashin dala bilyan 30 da ake bin Najeriya.
Sai kuma ga shi a wannan karo, ministocin sun sake bijiro da wannan batu a zaman su da kwamitoci, tare da bayyana dalili da fa’idar bukatar ciwo bashin cikin gaggawa.
Sun hakikice cewa idan aka ciwo bashin, za a gina kayan more rayuwa da kuma samar da aikin yi ga dimbin jama’a.
Ministar Harkokin Kudade cewa ta yi Najeriya na fama da rashin samun wadatattun kudaden haraji, don haka sai an maida hankali wajen gina ayyukan da za su kawo wa kasar nan kudaden shiga.
“Za a kashe kudaden ne kawai wajen gina ayyukan raya kasa. Ba za mu taba yarda ko kobo daya ya salwanta ta wata hanya, ba tare da an kashe shi ta hanyar ayyukan raya kasa ba.” Inji Zainab, Ministar Harkokin Kudade.
Da ya ke jawabi, Fashola ya ce shekara hudu kenan mu na gabatar da kasafin kudai, amma ba mu taba karba ko samun isassun kudaden da za a gudanar da ayyukan da ke shimfide a kasafin kudin ba. Saboda babu kudin, shi ya sa a duk shekara ake samun gibi, maimakon a samu rara.
“Idan mu ka samu kudaden yin ayyuka, to za a dade ana cin moriyar misali titina kusan har nan da shekaru 20 ko talatin ba su lalace ba.
Hanyoyin jiragen kasa kuwa, idan muka samu kudaden gina su, sai su shekara 100 ba su lalace ba. Haka aikin wutar lantarki na Mambila, zai dauki shekaru da dama ana cin moroyar sa, idan aka samu kudin yin aikin.”
Yayin da Fashola ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa don tuwon gobe suke son wanke tukunyar ciwo bashi tun a yau, ita kuma Gbemisola Saraki cewa ta yi, akwai bukatar ciwo bashi matuka domin a yi aikin titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano da ma wasu garuruwa.
Discussion about this post