Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya sallami malamai 200 dake aiki a makarantun Boko a karamar Hukumar Bama a dalilin kaurace wa aiki da suka yi har na tsawon shekara 1.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ziyarar aiki da ya kai karamar hukumar Konduga a cikin wannan mako.
A ranar Asabar din da ya gabata Zulum ya ziyarci karamar hukumar Kala Balge domin yi wa mutanen garin jajen fama da ambaliyar ruwa da suke fama da shi watanni hudu kenan.
Zulum ya raba wa mutanen garin kayan agaji da yada ada abinci, kayan sawa da sauran su.
Daga Rann sai gwamna Zulum ya zarce zuwa karamar hukumar Bama, inda a nan ne ya taras cewa daga cikin malamai 300 dake koyarwa a makarantun karamar hukumar, malamai 100 kawai ke zuwa aiki.
Zulum yace bayan an yi bincike gwamnati ta fatattake su sannan ta maye gurbin su maza-maza da sabin.
Sai dai kuma binciken UNESCO da aka gabatar a 2018 ya nuna cewa tun da rikicin Boko Haram ya kunnu kai a shekarar 2009 jihar ta rasa malamai 2,300.
Binciken ya kuma nuna cewa malamai 19,000 sun zama ‘yan gudun hijira.
Shugaban kungiyar malaman Najeriya (NUT) Jibrin Mohammed bai ce komai ba akan wannan abu da gwamna Zulum ya yi