Wasu likitoci a kasar Amurka sun bayyana cewa za a iya amfani da fitsarin mutum wajen gwada ko ya na dauke da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.
Likitocin sun ce wannan hanyar yin gwaji da suka gano na da saukin amfani sannan ko a gida ma mutum zai iya gwada kansa da shi.
Sun ce baya ga nuna ko mutum na dauke da cutar sakamakon gwajin na nuna matsayin da cutar ya kai a jikin mutum.
Likitocin sun ce amfani da wannan dabara zai taimaka wajen kare maza daga kamuwa da wannan cuta ganin cewa da zarar an gano za a iya warkewa daga ciwon idan har dai an gano da wuri.
Ciwon dajin dake kama ‘ya’yan maraina ciwo ne da ya fi kama bakaken fata maza a duniya kuma a lokutta da dama akan rasa rai idan ba a maida hankali a akai ba.
Ciwon baya tuna nuna alamun kamuwa da wuri a fili sannan har yanzu ba a iya gano takamamman abin da ke haddasa wannan ciwo ba.
Likitoci sun ce ciwon na kawo kumburin kafa, hana iya fitari, rashin iya saduwa da mace a ko da yaushe.
An shawarci maza da su yawaita zuwa yin gwaji musamman idan suka fara jin ba dai dai ba a mafitsaran su.