BAKON DAURO: Mutane sama da 140,000 sun rasu a kasashen duniya – Bincike

0

Sakamakon binciken kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ya nuna cewa mutane sama da 140,000 ne suka rasu a dalilin kamuwa da bakon dauro a kasashen duniya.

Binciken wanda aka gudanar a shekaran 2018 ya nuna cewa yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar ne suka fi mutuwa.

Shidai bakon Dauro cuta ce da allurar rigakafi ne kawai ke iya kawar da shi. An dai fi fama da wannan cuta ne a kasashen Afrika a dalilin rashin maida hankali da kasahen ba su yi wajen tilasta iyaye suna kai ya’ayn su ayi musu rigakafi.

A lissafe dai kasashen jamhuriyyar Kongo, Liberia, Madagascar, Somalia na daga cikin kasashen Afrika da wannan cuta ta yi wa katutu.

Idan ba a manta ba a watan Agusta ne hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta bayyana cewa yara sama da miliyan 26 a jihohi 25 da babbar birnin tarayya Abuja na cikin hadarin kamuwa da cutar bakon dauro a Najeriya.

A dalilin haka kuwa gwamnati a watan Nuwamba ta yi wa yara sama da miliyan 28 a jihohin arewa 19 a kasar nan allurar rigakafi cututtukan bakon dauro da sankarau.

Allurar rigakafin ya gudana ne a jihohin Bauchi, Benue, Borno, Kano, Katsina, Plateau, Taraba, Niger, Adamawa, Kaduna da Sokoto. Others are Gombe Jigawa, Kebbi, Nasarawa, Yobe, Zamfara, Kwara da babban birnin tarayya Abuja.

Share.

game da Author