Duk da irin gwagwagwar yakin Boko Haram sa sojojin Najeriya ke yi, Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da kafewa cewa ta na nasara a kan yaki da ‘yan ta’addar.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, yayin da ya ke karanta jawabi a taron manema labarai na karshem shekara a Lagos.
Lai ya jaddada irin namijin kokarin da jami’an sojojin Najeriya suka yi cikin shekarar 2019 wajen yaki da Boko Haram, ISWAP, masu garkuwa da mutane, mahara da sauran masu tayar da kayar baya.
Ya ce ko shakka babu an samu galaba a kan Boko Haram, ta yadda a yanzu sun kasa kai hare-hare a wasu garuruwa kamar yadda suka rika kaiwa a Arewacin kasar nan, har da Abuja.
Ministan Yada Labarai ya ce a yanzu Boko Haram saura ‘yan tsirarun da ke kai hare-haren sari-ka-noke daga tsibirin Tabkin Chadi.
Sannan kuma kamar yadda ya kara yin bayani, Boko Haram ba su rike da yankuna ko daya a hannun su.
“Tabbas an samu galabar dakile su wuri daya, sun daina ko na ce ba su iya kama wani gari ko yanki su kafa tuta kamar yadda suka yi a Bama can baya da ma wasu garuruwa.
“Duk wannan yanzu ya zama tarihi, domin a yanzu Boko Haram ba su iya kama gari su tsige sarkin gari su nada na su, balle har su rika karbar haraji daga jama’ar yankunan da suka mamaye.”
Za a iya cewa ana cin galaba a kan su, domin ko cikin makon da ya gabata an kashe 48. Sai dai kuma cikin 2019 Boko Haram sun yi wa sojojin Najeriya mummunar barna, inda suka rika kai masu hare-hare a sansanoni daban-daban a Barno da Yobe.
Ita dai gwamnatin tarayya na kan bakan ta cewa ta gama da Boko Haram wadda Shekau ke shugabanci. Yanzu ana yaki ne da ISWAP, wadda ke da tushe daga kasashen Larabawa.