Kamun da aka yi wa tsohon ministan shari’a na Najeriya, Mohammed Adoke a Dubai, ya bar baya da kura a Najeriya.
An kama Adoke ranar 11 Ga Nuwamba, amma kuma makonni uku kenan bayan an kama shi, Ministan Shari’a Malami, ya yi ta jajircewa ya na cewa hukumomi a Dubai ba su sanar da shi kamun da aka yi wa Adoke ba.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta bankado cewa sau biyu lauyoyin Adoke na aika masa wasikar sanarwa kamun da aka yi wa wanda suke karewa. Tun ranar 14 Ga Nuwamba suka fara sanar da Malami.
Wata majiya ta sanar da PREMIUM TIMES kamun da ‘yan sandan kasa-da-kasa suka yi wa Adoke tun a ranar 17 Ga Nuwamba, kwanaki shida bayan damke shi.
An ce an kama shi ne sakamakon binciken da ake ci gaba da yi dangane da dala bilyan 1.3 da aka karkatar na harkallar Rijiyar Mai da aka fi sani da Harkallar Malabu Oil.
.
An dai kama Adoke a Dubai, lokacin da ya isa domin likitocin sa su duba lafiyar sa, bayan da Najeriya ta yi watsi da sammacin da a farko ta fara rabawa a duniya, cewa duk inda aka gan shi, to a damke shi.
Ba a dai san ko daga wace kasa Adoke ya isa Dubai a ranar Litinin din sa aka kama shi ba. Sai dai kawai, an san ya tsere a kasashen waje ya na gudun hijira, tun cikin 2015, bayan kayar da gwamnatin Goodluck Jonathan a zabe.
Adoke ya ce ya arce ne saboda gwamnatin Najeriya na kokarin yin amfani da batun cinikin Malabu Oil ya bata masa suna.
A baya dai tuhumar da kotu ke yi wa Adoke dangane da harkallar Malabu Oil, ta samu cikas saboda jami’an tsaro sun kasa samun yadda za su aika masa da sammacin kotu da kuma kwafen ntakardun da ke dauke da bayanan tuhumar da ake yi masa.
Cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai Mai Shari’a Danladi Zenchi na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bai wa jami’an EFCC sammacin kamo Adoke.
An bayar da sammacin ne a ci gaba da binciken wadanda ke da hannu a harkallar Malabu Oil, wadanda suke hada da kamfanonin Shell da Eni, jami’an su da kuma wasu rubabbun manyan ‘yan siyasar Najeriya.
Sai dai kuma duk da cewa Adoke ya fice daga Najeriya tun bayan zaben 2015, har yau lauyoyin sa na ta hakilon kare shi a kotu nan Najeriya.
A kotu, lauyoyin Adoke sun shigar da karar neman a soke sammacin da aka bayar na kamo Adoke, domin a cewar su, babu sahihan hujjojin da ke nuna cewa Adoke na da hannu a harkallar Malabu Oil.
A ranar 25 Ga Oktoba, 2019, Mai Shari’a Zenchi ya soke sammacin da ya bai wa EFCC na iznin kamo Adoke. Amma ya ce a aika masa da sammacin kiran sa kotu, ba wai a kama shi da karfin iko a gurfanar da shi ba.
Soke sammacin iznin kama Adoke ya ba shi karfin guiwar ci gaba da zirga-zirgar sa kasashe, kamar yadda a baya ya rika yi.
Sai dai kuma ba zato ba tsammani ya na dira Dubai a ranar 11 Ga Nuwamba, sai ‘yan sandan kasa-da-kasa suka yi cacukui da shi, suka damka shi ga hukumar ‘yan sandan Dubai.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa EFCC ta rika aiki a boye tare da hadin bakin wasu jami’an tsaro na wasu kasashe, ciki kuwa har da Dubai, domin a kama Adoke.
Sai dai kuma tun bayan kama Adoke din, har yau EFCC ba ta fitar da wani jawabi dangane da damkewar da aka yi masa a waje ba. PREMIUM TIMES ta kasa samun Kakakin EFCC, Wilson Awujeran domin jin karin bayanin sa.
Idan ba a manta ba, cikin 2017 Malami ya shawarci Buhari cewa a yi watsi da tuhumar da ake yi wa Adoke da tsohuwar ministar harkokin mai Diezani Maduekwe a ma wasu, kan zargin su da harkallar Malabu Oil, domin babu wasu hujjojin da suka tabbatar da hannun su a ciki.
Sai dai kuma Hukumar EFCC ta kekasa kasa ta ki amincewa da wannan roko da Adoke ya yi wa Buhari, na neman a yi watsi da tuhumar.
Ofishin Ministan Shari’a Malami ya fitar da sanarwa a ranar 18 Ga Nuwamba, mako daya bayan damke Adoke cewa ba a sanar da Malami batun kama Adoke din ba.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta samu kwafen wasikar da babban lauyan Adoke, Mike Ozekhome ya rubuta wa Malami a ranar 14 da kuma 21 Ga Nuwamba, ya na neman ya jaddada batun soke sammacin neman kama Adoke da Mai Shari’a Zenchi ya bayar a cikin Oktoba, domin jami’an ‘yan sandan Dubai su saki Adoke din.
Lauyoyin Adoke sun nemi Malami ya rubuta wa mahukuntan Dubai wasikar neman su saki Adoke, saboda kotu ta soke sammacin da aka bayar cewa a kama shi.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Malami, amma bai ce mata ko uffan ba.