Dan sanda ya bindige wani direban tirela a kan cin hancin da suke karba na naira 50, a hanyar Akure zuwa Owo, cikin Jihar Ondo.
PREMIUM TIMES ta gano cewa diraban da aka bindige har lahira, mai suna Ado Saleh, an dirka masa bindiga ne saboda ya ki bayar da cin hanci na naira 50, a shingen da ‘yan sanda suka yi kan babban titin, su na karbar kudade daga hannun direbobi.
Kisan da dan sanda ya yi wa direban, ya haifar da zanga-zangar da ta yi sanadiyyar rufe titin, gaba daya ba a wucewa.
Wanda aka bindige direban a gaban sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kin bayar da kyautar naira 50 ga ‘yan sanda ya haifar da sa-in-sa tsakanin dan sandan da kuma Saleh.
“Ana cikin hayaniya ne wani dan sanda ya saita shi da bindiga, ya dirka masa harbi.” Haka wanda aka yi harbin a gaban say a tabbatar.
Wani shi ma da aka yi harbin a gaban sa, ya ce Salah a nan take ya mutu, a wurin da aka harbe shi.
Wannan harbi ya janyo jama’a suka fara zanga-zanga, wadda ‘yan sanda suka kasa kwantarwa.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES afkuwar lamarin, tare da cewa “abin bakin ciki da takaici ne matuka.”
“Mutuwar wannan mutum da aka ce an harbe, abin bakin ciki ce matuka. Mu na mika ta’aziyyar mu ga iyayen sa da iyalan marigayi Ado Saleh.
“Daga nan sai ya roki jama’a kada su yi amfani da danyen aikin da dan sanda daya ya yi su yi wa sauran ‘yan sanda kudin-goro cewa duk haka suke.
“Mu na nan mu na binciken lamari, tare kuma da shaida wa jama’a cewa jami’an ‘yan sanda na kaunar su matuka.”
Da PREMIUM TIMES ta tambaye shi sunan jami’in dan sandan da ya dirka wa direban harbi, sai ya ce a’a, ba zai bayyana ba, saboda har yanzu ana cikin bincike.
“Mu na kan bincike, amma dai tabbas ina sanar da ku cewa za a hukunta wanda aka kama da laifin kisan, daidai da irin hukuncin laifin da ya aikata.”
Discussion about this post