GIDOGAR KASAFIN 2020: Naira Bilyan 37 don kwaskwarimar Majalisa sun zarce kudin gyaran titinan Najeriya

0

A zaman da ake ciki yanzu haka, Najeriya ta shirya tsaf za ta kashe zunzurutun kudi har naira bilyan 37, domin yi wa ginin Majalisar Tarayya kwaskwarima.

Hakan ya tabbata ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kasafin 2020 jiya da yamma.

Za a kashe kudaden ne bayan da Majalisa ta karbi kasafin kudin daga Majalisar Dattawa, wadda ta kara narka kudaden ayyuka har na naira bilyan 264 da Buhari bai san da su a lokacin da ya damka musu kasafin kudin ba.

Yanzu dai wadannan makudan kudade har naira bilyan 37 da za a kashe wajen gyaran wurare gine-gine a Majalisa, har sun zarta wadanda Shugaba Buhari zai kashe a fannin gyaran titinanan kasar nan kakaf a cikin shekarar 2020.

Buhari ya amince a kashe wadannan makudan kudade a Majalisar Dattawa da ta Tarayya a jiya Litinin bayan da Shugabannin Majalisa, Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila sun gana da shi, inda suka nuna masa muhimmanci ko wajibcin kashe makudan kudaden wajen yin gyare-gyaren.

Batun kashe wadannan makudan kudade dai ya fusata mafi yawan ‘yan Najeriya tun daga jiya Talata, inda ake ta yin tir da batun, tare da cewa alkawarin kawo canji da tsantsenin kashe kudade da Buhari ya yi, duk ya zama tatsuniya kenan.

Da dama kuma na cewa da a ce majalisar zamanin Bukola Saraki ce za ta kashe naira bilyan 37 wajen yi wa gini kwaskwarima, tuni da an yi ta tsine masa ana yi masa Allah-wadai.

Wani abin mamaki shi ne yadda kasafin gyaran titinan kasar nan da aka ware wa Hukumar Gyara da Kula da Titina ta Kasa (FERMA), bai kai na kudaden kwaskwarimar ginin majalisa ba.

An dai ware wa FERMA nai bilyan 36.6 ne a matsayin kudaden gyara titinan Najeriya a cikin 2020.

Karin abin daure kai shi ne wadannan kudaden gyaran majalisa, kwata-kwata ba su fa cikin kasafin naira bilyan 128 da aka ware wa Majalisaun biyu a 2020.

Abin daure kai shi ne yadda aka cusa wadannan naira bilyan 37 a cikin Kasafin Abuja, FCDA, wadda aka ware wa naira bilyan 62.4.

Hakan na nufin kenan daga cikin naira bilyan 62.4 da aka ware wa FCDA, sama da rabin kudaden duk za a karkatar da su wajen kwaskwarimar ginin majalisa kenan. Sauran kudaden da suka rage ne za a yi wa Abuja gaba dayan ta aiki da su.

Share.

game da Author