Mutuwa ta ratsa cikin Majalisar Dattawa, ta dauki ran Sanata

0

A yau Laraba da safe na aka bada sanarwar rasuwar Sanata Ben Uwajumogu.

Sanatan ya rasu a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda shakikin makusancin sa, Sanata Elisha Abbo ya bayyana.

Uwajumogu ya rasu ya na da shekaru 51 a duniya.

“Ina sanar da ku cewa abokin aiki na kuma dan uwa na, Sanata Ben Uwajumagu ya koma ga mahaliccin sa a yau.” Haka Sanata Abbo ya shaida wa Premium Times a yau da rana.

Ya ce su na cikin halin jimami da alhinin wannan babban rashi.

“Rasuwar sa ta kara nuna mana cewa wannan duniya tamkar cin kasuwa ce, inda kowa zai watse ya koma gida idan kasuwa ta tashi.

“Kowa zai koma ga ubangijin sa, ya dauki nauyin duk abin ya aikata a nan duniya.” Inji Sanata Abbo.

“Uwajumogu dan jam’iyyar APC ne, wanda da farko ya yi jiyya a Dubai, amma da aka ga alamun sauki da murmurewa, sai aka sallame shi, ya dawo Abuja. Haka wata majiya da ke kusanci da iyalan sa ta shaida wa wakilin mu.

Har yanzu dai Majalisar Dattawa ba ta sanar da rasuwar sanatan ba, amma daya daga cikin manyan hadiman Shugaban Majalaisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an sanar da Lawan rasuwar, kuma za a fitar da bayani daga majalisar nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author