GWAMNONIN AREWA A 2019: Wane Ne Gwarzon Ku, Wane Ne Gwangwani?

0

Kamar yadda bankuna da kamfanoni ke rufe karshen kowace shekara da kididdigar ciniki, riba, faduwa ko narkewar jari a tsawon hada-hadar shekara daya. To kamar haka nan ita ma PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo wa masu karatu jerin wasu gwamnonin Arewa 5 da ake ganin sun fi saura tabuka abin-kwarai ko akasin haka a cikin 2019.

“Cikin maza ake samo namiji”, haka dai Musa Dankwairo ya yi wa marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Ado Bayero kirari. To haka mu ke so masu karatu su fitar da gwarzo daya daga cikin wadannan gwarzayen gwamnoni biyar.

Mai karatu, wane gwamna ne namijin gwamnoni daga cikin su?

Mai karatu zai iya fitar da gwanin sa ko da ta hanyar zaben wanda aka fi yada labarin sa ko labarin jihar sa ne a cikin 2019, ba sai wanda ake ganin ya fi sauran aiki ba.

Gwamna Matawalle: Sha-yanzu-magani-yanzu

Kamar yadda allurar ‘zalaken’ ke saurin kashe jiki yadda ba za a ji ciwo idan za a yi wa majiyyaci tiyata ba, haka Bello Matawalle ya magance bala’in garkuwa da mutane da kashe-kashen da aka rika fama da su a Jihar Zamfara. Abin da gwamnatin baya ta kasa magancewa cikin shekaru 10, Matawalle ya shawo kan sa cikin watanni hudu.

Matawalle ya fito da dokokin da sai namijin kwarai ne zai iya fito da su a karkashin gwamnatin siyasa.

Gwamna Babagana Zulum: Aiki ga mai kare ka

Farkon abin da ya fara yi a hawan sa shi ne tabbatar da cewa ya saisaita tsarin ma’aikatan gwamnatin jihar. Ya hana zuwa a makare, ya hana fashi, kuma ya hana ma’aikacin gwamnati zaman dirshan a ofis. Ko dai ka kama aiki, ko a tilasta ka kama aiki ko kuma ka kama hanyar gida.

Zulum ba ya zullumin bayyana gaskiyar magana yadda ta ke. Ko cikin wannan makon ya yi kira ga sojoji su kwato Karamar Hukumar Kukawa daga hannun Boko Haram.

Sannan kuma ya sha zuwa garuruwan da ake tsoron zuwa ya na kwana a can ko ma shafe kwanaki. Lallai ‘matsoraci ba ya zama gwani’, kamar yadda marigayi Shata ya fadi a cikin ‘Bakandamiya.’

Zulum ya maida hankali wajen kafa Cibiyar Kula da Masu Ciwon Koda da sauran ayyukan da ya sa gaba a cikin kankanin lokaci.

Gwamna Ganduje: Gandun Aiki ko Gandun Aika-Aika

Duk da makudan dalolin da aka nuno shi ya na dankarawa aljihu, wannan bai hana magoya bayan sa kiran sa ‘Khadimul Islam’ ba, saboda taimakon da suke ganin ya na yi wa adddinin Musulunci a 2019.

Ganduje ya fasa Masarautar Kano, inda ya raba ta gida biyar. Wannan ya janyo masa farin jini da kuma bakin jini. Ya gina gadar-sama ya sa mata sunan Karibullah Nasiru Kabara. Ganduje ya zama guga ba ki tsoron rami. Ya zama margamargan dutse ka fi gaban aljihu. Sannan kuma ya zame wa Kano wani biri da gatari, mai kashe mai gona. Duk a cikin 2019.

Gwamna El-Rufai: Raina kama ka ga gayya

Sai mutum ya rasa irin lakabin da ya dace ya rada wa El-Rufai suna da shi. Ko ka kira shi ‘kiyashi dauki abin da ya fi ka karfi’, ko ‘gajere ka ki a fi ka’ ko ‘wukar yanka giwa, kaifi gare ki ba girma ba.’

El-Rufai a cikin 2019 ya yi abin da jama’a da dama ke tunanin ba zai yiwu ba, amma shi ya yi hakan kuma ta kai masa, har ma an wuce wurin.

Ya tsaida mace mataimakiyar gwamna. Ya yi nasara, an wuce wurin. Ya hana Kiristocin Kaduna tsaida mataimakin gwamna. Tuni an wuce wurin. Ya barko ayyukan titina a Kaduna, ya na rushe duk wani gini ko gidan da ya tare masa gaba. Sannan kuma ya sa takalmin karfe ya taka duk wanda ya tare masa hanya. Kuma wanda ya taka ya taku.

Malam, kamar yadda ake kiran sa, ya yi amfani da kaifin askar kuri’u ya aske gashin kan Sanata Shehu Sani, sannan ya aske gemun wani babban dan siyasar jihar, kuma an wuce wurin. Wa zai iya yi wa Kudanci da Arewacin Kaduna hawan-kawara in ba Nasir ba? Sannan kwanan nan ya bugi kirjin nasarar da ya samu a fadan sa da ‘yan Shi’a.

Gwamna Yahaya Bello: Gobara daga Kogi

Babu wanda ya taba tunanin Gwamna Yahaya Bello zai zama wani babban gogarman iya kwatar wa kan sa kujerar gwamna a jihar Kogi, a zaben cikin watan Nuwamba, 2019.

Dalili, ana ganin shi ne gwamnan da ya fi kowa rashin tabuka abin kirki a tsawon shekaru hudu da ya yi ya na mulki.

Ya sa an tsige mataimakin sa, kuma ya kwana lafiya. Bello ya samu tagomashin karbar naira bilyan 10 a jajibirin zaben gwamna. Ya shafe watanni ba ya biyan albashi. Bai yi abin kirki a jihar ba. Amma hakan bai hana gwamnatin Buhari taya shi neman sake nasara a zaben gwamna karo na biyu ba.

An aikata duk wasu laifukan da INEC ta haramta aikatawa a lokacin zabe a jihar Kogi. Har ta kai an kone wata jigon jam’iyyar PDP a jihar Kogi, amma duk wannan bai hana hatta Shugaba Muhammadu Buhari taya shi murnar ‘nasarar kayar da abokan hamayya’ ba.

Bello ya fi dukkan sauran gwamnonin kasar nan karancin shekaru. Amma ya nuna wa sauran cewa ko a cikin wuta ake zabe, zai iya shiga ya fito rungume da kujerar sa, ko da kuwa za ta tafasa ta kone.

Wane Ne Gwanin Ku?

Masu karatu, wane gwamna ne ya yi kamar yadda Matawalle ya yi a 2019? Wane gwamna ya yi kamar yadda Zulum ya yi a 2019? Wane gwamna ne zai iya yin yadda El-Rufai ya yi a 2019? Wane gwamna ne zai iya yin kamar yadda Ganduje ya yi a 2019? Wane gogarman gwamna zai iya yin yadda Bello na Kogi ya yi a cikin 2019?

To kowa dai ya zabi daya tal, a ga wanda zai yi nasara.

Hausawa dai sun ce, “ranar naka sai naka.”

Share.

game da Author