Boko Haram sun kashe amarya da kawayenta a kusa da garin Gwoza

0

Boko Haram sun kashe wata Amarya da kawayenta a hanyarsu na zuwa garin Yola daga Maiduguri inda za a daura mata aure.

Amaryar mai suna Martha Bulus tare da kawayenta sun shiga mota ne a tashar Bama dake Maiduguri zuwa Yola, jihar Adamawa.

Bayanai dai sun nuna cewa gaba dayan su wato Amarya Matha da kawayenta Boko Haram suka kashe.

Boko Haram sun bude wa motan da wadanan amare suke wuta ne a kusa da garin Gwoza, wato titin Maiduguri zuwa Gwoza.

Za a daura wa Matha aure da masoyinta Joseph Zamdai a makon gobe a garin Yola, ranar 31 ga watan Disamba.

A dalilin haka ne ya sa suka dunguma zuwa garin Yola domin shirye-shirye ganin cewa aski ya zo gaban goshi.

Yan uwa da abokan arziki duk sun yi turuwa a shafunan wadanda aka rasa suna ta yi musu addua’ar Allah yayi musu makwanci mai kyau.

Share.

game da Author