Kano ta cika ta batse ranar Juma’a a dalilin daurin auren babban dan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawal, Ibrahim Ahmad da aka yi a garin Kano.
An dai fara shgulgulan bikin ne tun ranar laraba da akayi kamu sannan aka ci gaba da sauran taron buki ranar Alhamis.
A yau Juma’a kuma aka daura a auren a masallacin Alfurqan dake Kano.
Babban malami kuma ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya bada aure a matsayin waliyin amarya Amani Bala Umar.
Gwamnan Yobe, Mala Buni kuma ya amshi aure a matsayin waliyin ango.
Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya da dama be suka halarci wannan bukin aure.