2019: Matsaloli 5 da suka kawo rudani a Kannywood

0

1 – Ali Nuhu ya Maka Adam Zango a Kotu

Na farko dai shine yadda rashin jituwa a tsakanin fitattun jaruman farfajiyar fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam Zango  ya kai kololuwa a shekarar 2019.

A wannan shekara gaba dayan su suka shata wa juna iyaka da yakai ga har suna ambatar sunayen juna sannan har ma Ali Nuhu ya maka Adam Zango a Kotu.

Hakan ya kai ga Adam Zango yayi sallama da Kannywood inda ya ce zai garzaya ya bude tasa farfajiyar fina-finan sannan ya zargi Ali Nuhu da zuga yaran sa a farfajiyar su rika yi masa rashin kun ya.

Sai da manya suka shiga cikin maganar sannan Ali Nuhu ya janye wannan kara da ya shigar a kotu.

2 – Kicimewar Zaharaddeen Sani da Ummi Zeezee

A shekarar 2019 ne aka kicime tsakanin jarumi Zaharadden  Sani da Ummi Zee Zee in da ta zargi Zaharaddeen da yin sama da fadi da kudaden alfarma da Atiku Abubakar ya rabawa Jaruman Kannywood.

Zeezee ta zargi Zaharaddeen, Sani Danja, Al’amin Buhari da laifin wawushe kudaden jyauta da aka basu su raba a lokacin kamfrn din zaben 2019 inda suka aika mata da wanda bai isa ta saka kati a waya ba.

Sannan ta yi musu kurin duk sai ta daure su a kurkuku badin an bata hakuri ba.

Zaharaddeen ya fusata, inda ya shigar da kara a caji ofis sannan ‘yan sanda suka fantsama neman ta kamar yadda Zaharaddeen ya ne mi a yi.

Tuni dai Zeezee ta ari na kare ta cika wa wandonta iska. Ba a samu dai an kai ga kamata ba har aka yi sulhu.

 3 – ZARGI: Yadda Hadiza Gabon ta rika sharara wa Amina Amal Mari

A shekarar 2019 an rika saka wani bidiyo da ke numa jaruma Hadiza Gabon na sharara wa Amina Amal mari tana zaune tana tilastata ta maida magana.

Hadiza ta zargi Amal da yi mata kazafi wai suna tarayya na tsananin kusanta.

Hakan bai yi wa Gabon dadi ba inda ta tarke ta a wani daki ta rika sharara mata mari tana cewa lallai sai ta maida ba’asin magana kokuma ta ci gaba da lakada mata dukan tsiya.

Duk da wani dake tare da su ya yi ta rokon Hadiza ta hakura amma ba a dace.

Shima dai sai da manya suka sa baki kafin aka samu aka daidaita su.

ADAM ZANGO: Zargin saka yara mata kanana a fina-finai

Idan ba a manta ba wani malami a wannan shekara ya fito kan mumbari ya kalubalanci Adam Zango da ya fito ya karyata zargin saka yara mata kanana a fina-finan sa da shi da kansa yake tallatawa.

Malamin ya soki wannan lamiri na Adam Zango inda ya ce abinda yake yi ba daidai bane kuma bata tarbiya ne da halayyar mutanen arewa da ci wa musulunci fuska.

Daga baya Zango ya fi cikin wani bidiyo da ya saka a shafinsa inda ya karyata malamin ya ce sharri yake masa.

Kai har Alkur’ani mai girma ya rantse da shi cewa shi ba abin da yake nufi ba ne wannan kira da yayi na masu sha’awar shiga fim din sa su garzayo a zabe su.

5 – Tir da shigan Rahama Sadau a bukin ranar Zagayowarta – Maisana’a

Jim kadan bayan ragargajewa da akayi wajen bukin zagayowar ranar haihuwar jaruma Rahama Sadau a garin Kaduna wasu daga cikin mutane har da abokan aikin ta suka rika sukar irin shigar da tayi a wajen wannan party.

Rahama ta yi shigar bariki, cikin jar doguwar riga, guiwowinta a waje sannan ta rika rangwada rawa abinta babu kakkauta.

Jarumi Maisana’a ya fito karara yana sukar wannan shiga da Rahama ta yi sannan ya gargade ta da kada ta kuskura ta zo garin Kano da irin wannan buki.

Share.

game da Author