Sakamakon binciken da wasu likitocin kasar Amurka suka yi ya nuna cewa amfani da man zaitun musamman wajen girki na taimakawa wajen inganta lafiyar kwakwalwar.
Binciken ya nuna cewa man zaitun baya daskarewa a jikin mutum kamar kitse wato ‘Protein Tau’ wanda likitoci suka ce yana haddasa cutar mantuwa wato ‘Dementia’.
Likitocin sun kuma gano cewa man zaitun na kara lafiyar jijiyoyi a jiki da kwakwalwa.
Sannan yana kara kyan fata da tsawon gashi a kai.
Bayanai sun nuna cewa yawan mantuwa bai tsaya ga tsofaffi ba yanzu har da yara kanana.
Sakamakon hakan ne ya sa masana suka yi wani nazari kan haka da gano abubuwan da zai iya sa mutum ya rage yawan yin mantuwa.
A binciken da masannan suka fara yi sun gano cewa shan kayan zaki kamar su alawa, cingam, chakulat da sauran su na taimakawa wajen kara kaifin kwakwalwa.
Da yake wasu ba za su iya mu’amala da wadan nan kayan zaki ba, an zurfafa bincike domin gano wasu hanyoyin.
Hanyoyin sun hada da;
1. Samun isasshen barci sannan da yin barci a lokacin da ya kamata.
2. Yin hirar zuci amma ba kowani lokaci ba domin yawan yin hakan na iya sa mutum ya sami matsala a kwakwalwar sa.
3. Yin hira da mutane musamman abokan arziki.
4. Motsa jiki kamar su guje-guje da sauran su.
5. Tsayawa a hasken rana wanda ke bada Sinadarin ‘Vitamin D’ sannan da cin kayan abincin kamar kayan lambu.
6. Yin wasannin wasa kwakwalwa kamar chess, Sudoku, lisafi da sauran su.
7. Yin aiyukkan da ba a saba yi ba ko kuma ba a taba yi ba da ziyarar wuraren da ba a taba zuwa ba.
8. Yawan yin dariya wanda hakan ke kawar da damuwa da dodewar kwanya.
9. Cin kayan lambu da ake kira ‘Bule Berries’ domin suna dauke da sinadarorin dake taimakawa wajen hana mantuwa.
Discussion about this post