RANAR KANJAMAU TA DUNIYA: Kare jarirai daga Kamuwa da Kanjama shine a gaban mu yanzu – Aliyu Gambo

0

Shugaban Hukumar NACA, Gambo Aliyu ya bayyana cewa babban abinda gwamnati ta sa a gaba yanzu shine ganin yadda za a dakile yawa-yawan samun jarirai da ake haihuwa dauke da Kanjamau a kasar nan.

Aliyu ya bayyana haka ne a wajen taron ranar Kanjamau ta Duniya da ake yi a irin wannan rana ta yau duk Shekara.

Ranar cutar Kanjamau ta duniya rana ce da aka kebe domin tunawa da mutanen da suka riga mu gidan gaskiya a dalilin cutar Kanjamau, mutanen dake dauke da cutar sannan da wayar da kan mutane game da cutar.

Wannan karon fannin kiwon lafiyar Najeriya ta maida hankali wajen kirkiro hanyoyin da za arika samar wa jarirai da ke cikin uwayensu kariya daga kamuwa da cutar.

Idan ba a manta ba a watan Maris hukumar NACA ta gabatar da sakamakon adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a kasar nan.

Binciken ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar sannan masu shekaru kasa da shekara 64 ne suka fi yawa a kasan.

Baya ga haka binciken ya nuna cewa daga cikin jarirai 160,000 masu dauke da cutar da ake haifowa a duniya 37,000 daga Najeriya suke.

Duk da haka a taron da aka yi a shekarar 2018 babban bako kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya bayyana cewa gwamnati za ta yi kokari wajen ganin ta dakile yawudar cutar kafin nan da 2030.

Osinbajo yace gwamnati ta ware makudan kudade domin ganin an inganta yin gwajin cutar,samar da kula ta gari wa mata musamman masu ciki domin kare jarirai daga kamuwa da cutar da sauran su.

Sai dai duk da haka Najeriya na samun jariran da ake haifa dauke da cutar.

RASHIN ISAR DA SAKON KANJAMAU GA MUTANE MUSAMMAN MAZAUNAN KARKARA.

Wani jami’in gidauniyar ‘AIDs Healthcare (AHF) Steve Aborisade ya ce kare jarirai daga kamuwa da kanjamau tun suna cikin mahaifan su zai yiwu ne a Najeriya idan gwamnati ta isar da sakon kanjamau ga mutane musamman mazauna karkara.

Aborisade y ace hakan ya shafi wayar da kan mutane musamman mazauna karkara game da cutar,inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake yankin karkara da rage farashin samun kiwon lafiya ta gari.

Daga nan shugaban hukumar NACA Aliyu Gambo ya ce gwamnati na kokarin shawo kan wannan matsala ne ta hanyar horar da unguwar zoman gargajiyya mahimmancin yi wa mata masu ciki da yara kanana gwajin cutar sannan da aikawa da wadanda ke dauke da cutar zuwa asibiti.

Ya ce haka zai taimaka wajen dakile cutar da gwamnatin ke da burin yin nan da 2030.

Share.

game da Author