Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Edo, Anselm Ojezua, ya bayyana cewa gwamnonin kasar nan da aka zaba a karkashin APC ba su da sauran daga wa Adams Oshiomhole kafa, duk su na goyon bayan a tsige shi daga shugabancin jam’iyyar na kasa baki daya da ya ke yi.
“Ba shi da sauran wani kwarjini ko martaba a idon gwamnonin APC. Duk suna ganin a tsige shi, amma kuma ba su son fitowa fili su nuna, gudun kada a ga kamar su ne ke sahun gaban hada tuggun tsige shi.
Ojezua ya kara da cewa “gwamnonin so suke Oshiomhole ya dau haske, ya sauka don kan sa, kada a kunyata shi a tsige shi.”
“Saboda ni dai ban ga yadda Oshiomhole zai iya tsallake wannan lokacin ba.” Inji shi.
Daga nan sai ya bada labarin abin da ya faru a wurin taron Kwamitin Zartaswa na APC, inda ya ce “Oshiomhole bai bari an yi taron kamar yadda ya dace kuma kamar yadda aka tsara gudanar da shi ba. Kawai sai ya rika bankaura da harmagaza, warware tabarmar kunya, kuma ya na nadewa a lokaci guda ya na nade tabarmar.
Ojezua shi ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Edo, mai goyon bayan Gwamna Obaseki, kuma jajirtaccen mai takun-saka da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole.
Cikin makon da ya gabata ne Babbar Kotun Jihar Edo ta haramta wa uwar jam’iyyar APC ta Kasa cire Ojezua daga mukamin sa na shugaban APC ta jihar Edo.
Rigima ta yi kamari a Edo, tsakanin gwamna Obaseki da tsohon ubangidan sa, Oshiomhole, har ta kai ga cikin watan jiya an yi wa gwamna kwanton bauna an jefi motar sa. Uwar jam’iyya dai ta kafa kwamitin sasanta su.