AIKIN GAMA: Buhari ya sa hannu kan Kasafin 2020

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa da kuma zartas da Kasafin Kudi na 2020 ya zama doka.

Ya sa wa kasafin na 2020 hannu ne a yau Talata, wajen karfe 3:30 na rana.

A ranar 5 Ga Disamba ne Majalisar Dattawa ta mika kasafin kudin, bayan ta yi masa cushe da azuraren ayyuka har na naira bilyan 264,
Buhari ya damka musu kasafin tun a ranar 8 Ga Oktoba, 2019.

Majalisar Dattawa ta kara kasafin daga naira tiriliyan 10.33 da Buhari ya kai mata, zuwa naira tiriliyan 10.50.

Wadanda suka halarci kwarya-kwaryan zaman sa wa kasafin hannu sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da kuma Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, Ministan Kasafin Kudade da Tsare-tsare, Clement Agba da kuma Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kudade, Ben Akabueze.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka “dankara cushen ayyuka na tsabar kudade har na naira bilyan 264, wanda hukumar dakile rashawa ta kira ayyukan gidoga da jidar kudaden azurta kawunan su da aka yi a Majalisa”.

Buhari ya sa wa Kasafin Hannu a ranar Talata, ranar da ya cika shekara 77 da haihuwa.

Share.

game da Author