Dimokradiyya ba ta burge ni saboda tafiyar hawainiya da ake yi a shari’u – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya tuna lokacin mulkin sa na soja, inda ya ke da cikakken ikon kafa doka nan take-yanke, kuma a daure mutum ba tare da bata lokaci ba.

Buhari wanda ya yi mulkin soja daga ranar 31 Ga Disamba, 1983 zuwa 26 Ga Agusta, 1985, ya yi wannan tuna baya ne a yau Talata, lokacin da ya ke wata tattaunawa da Gidan Talbijin na NTA, dangane da zagayowar ranar haihuwar sa.

A yau ne Buhari ya cika shekaru 77 a duniya. Ya bayyana wa NTA cewa ba ya jin dadin yadda tsarin shari’a ke tafiyar hawainiya a karkashin mulkin dimokradiyya.

“Lokacin da ina mulkin soja a cikin kaki, na tattara shugabanni na garkame a Kurkukun Kirikiri, kuma na ce musu duk ba su da gaskiya. Wanda ya ke da hujjar bai aikata laifin da aka tuhume shi ba, to ya zo da hujja.”

Buhari ya nuna rashin jin dadin yadda irin haka ba za ta iya faruwa a mulkin dimokradiyya ba.

“A lokacin na kakkafa kotunan bincike domin binciken wadanda na kama na daure. Wadanda aka samu da tara dukiyar da ta wuce adadin gwargwadon sanmun su, an kwace an maida kudaden a aljihun gwamnati.

“To amma da ta juya ta juyo, ni ma din sai da aka tsare ni.”

“A yanzu ba ni da wani zabi sai na bi wannan tsari na dimokradiyya, wanda ni dai ba son yadda ake jan-kafa da hawainiya wajen gudanar da shari’a na ke yi ba. Saboda tsarin ba ya birge ni.” Inji Buhari.

Share.

game da Author