Za a samu karin yawan mutane da za su rika yin gwajin kamuwa da ‘ciwon sanyi’ a duniya.
Sakamakon binciken da kamfanin ‘Technavio’ ta gudanar ya nuna cewa nan da shekaru biyar masu zuwa ciniken kasuwan da ake samu a yi wa mutane gwajin cutar sanyi zai karu a duniya.
A lissafe dai binciken ya nuna cewa za a samu karin dala biliyan 73.59 daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Kamfanin Technavio kamfani ce da ta kware a gudanar da bincike dake da hedikwatarta a kasar Birtaniya.
Bayan haka binciken ya kuma nuna cewa yankin Amurka ta Arewa ce za ta fi samun babban kaso a wannan ciniki a saboda kwarewa wajen gwaji da samar da ingantattun magunguna da wannan yanki ke dashi.
Idan ba a manta ba a shekaran 2017 kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gargadi mutane da su yi kaffa-kaffa da kamuwa da cutar sanyi wato ‘Gonorrhoea’ domin yanzu cutar bata jin magani.
Kungiyar WHO ta yi wannan shela ne don wayar da kan mutane sannan da tunashe su game da hadarin dake tattare da cutar musamman ganin maganinsa yayi wuya.
Ita dai wannan cutar sanyin da ake kira da ‘Gonorrhoea’ wata bacteria ce ke kawo ta mai suna ‘Neisseria gonorrhoeae ko kuma gonococcus’ wanda ke kama al’auran namiji ko mace.
Daya daga cikin alamonin cutar da ake iya gani idan an kamu shine yadda gaban namiji ko mace zai dunga fitar da farin ruwa wanda wata sa’an yakan yi wari sannan kuma an fi kamuwa da cutar ta hanyar saduwa da juna.
Kungiyar ta kuma gano a wani binciken da ta yi cewa a duk shekara mutane miliyan 78 na kamuwa da cutar; kasan Biritaniya kuwa ta ce kashi 10 bisa 100 sun kamu da cutar a shekaran 2015 sannan a kasar Faransa mutanen da ke aikata luwadi sun fi yawa cikin wadanda ke dauke da cutar a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015.
Kungiyar ta kara da cewa kasashen yankin Afrika sun fi yawa domin cikin mutane 10 mutum daya na dauke da cutar.
Kungiyar WHO ta bayyana wasu dalilan da ke kawo yaduwar cutar wanda ya hada da rashin amfani da kwarroro roba lokacin da za a yi jima’I da kuma rashin yin gwaji kan.
Baya ga haka dakta Daivi Bawa ya yi kira ga mata da su yi kafa-kafa wajen kare kansu daga kamuwa da cutar sanyi.
Bawa ya fadi haka ne saboda mata sun fi maza kamuwa da cututtuka itin haka.
Ya ce a halicce al’auran mace a bude yake sannan bashi da kariya kamar na namiji wanda hakan ya sa cututtuka ke saurin shiga jikin su.
A dalilin hakan ya sa yake kira ga mata da su dunga kare kansu ta hayar guje wa amfani da bayi mara tsafta, wanke gaban su da sabulu, fesa turare a gaban su domin yin hakan zai kare su daga kamuwa da cututtuka da ya hada da cutar sanyi.