Abin da ya faru da ni daga Allah ne, babu kullalliya tsakani na da Buhari – Inji Dasuki

0

Tsohon mai ba tsohon shugaban kasan Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, ya bayyana cewa ba ya gaba da kowa sannan abinda ya auku da dashi na tsare shi da aka yi na tsawon shekaru 4 daga Allah ne amma baya gaba da kowa.

Dasuki ya yi wannan bayani ne da ya ke hira da Muryar Amurka ranar Laraba.

Dasuki ya bayyana cewa ya mika dukka al’amuransa ga Allah ne sannan ba ya ganin wani ya isa yayi masa wani abu idan ba daga Allah ba.

Da aka tambaye shi ko akwai wata kullalliya tsakanin sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a bisa cewa da akeyi wai yana daga cikin wadanda suka kamo shi alokacin da Janar Ibrahim Babangida yayi masa Ku’. Dasuki ya ce babu abinda zai ce akan haka duk abinda ya faru dai daga Allah ne kuma shine mai iko akan komai.

” Shekaru na hudu a tsare amma yanzu gashi Allah yayi an sake ki. Ina matukar godiya ga Allah. Sannan bani da wata kullaliya tsakani na da shugaban kasa Muhammadu Buhari kai da kowa ma, ni lafiya lau nake.”

Da aka tambaye shi ko zai ci gaba da zuwa kotu domin wanke kansa game da abin da ake tuhumar sa sai ya ce tabbas zai je domin ya wanke kansa. ” Da ma can na dai na zuwa kotu domin an bada beli na amma yanzu tunda na fito, dole in garzaya in wanke kai na.”

Share.

game da Author