Bayan shafe shekaru hudu da ya yi yana tsare hukumar tsaro na SSS ta sake Sambo Dasuki cikin daren Talata.
Hakan ya biyo bayan umarnin da Antoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami ya baiwa hukumar SSS da ta saki Sowore da Sambo Dasuki.
Lauyan Dasuki, Ahmed Raji ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa SSS sun saki Dasuki a yau Talata.
Idan ba a manta ba a yammacin Talata ne hukumar SSS ta sanar da shirin sakin tsohon maiba shugaban kasa shawara kan harkokin Tsaro, Sambo Dasuki a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da mawallafin jaridar Sahara Reporters da duk ke tsare.
Hukumar ta gayyaci lauyoyin Dasuki da Sowore su garzayo ofishinta maza-maza domin cika takardun sakin su.
Hukumar SSS ta tsare Dasuki tun a watan Disambar 2015 a bisa zargin harkallar dala biliyan 2 kudin makamai a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Bayan haka duk a yau din hukumar SSS din ta saki mawallafin jaridar Sahara da ke tsare a hannun hukumar Yele Sowore.
An saki Sowore da misalin karfe shida na yammacin Talata a Abuja.