Saudiyya ta haramta auren budurwar da ba ta kai shekaru 18 ba

0

Ma’aikatar Shari’a ta Saudiyya ta bayyana sanarwar haramta aurar da yarinya har sai ta kai shekaru 18 abin da ya yi sama.

Kamar yadda jaridun kasar, ciki har da Saudi Gazette da Arab News suka ruwaito, sun bayyana cewa Ma’aikatar Shari’a ta Saudiyya ta shata ka’idar cewa sai budurwa ta cika shekaru 18 cif sannan za a daura mata aure.

Wannan ya na nufin kasar ta haramta auren duk budurwar da ba ta kai shekaru 18 ba kenan.

Ministan Shari’a kuma Shugaban Majalisar Alkalan Saudiyya, Sheikh Walid Al-Samaani ne ya fitar da wannan sanarwa mai dauke da sa hannun sa a yau Talata.

An kuma tura wannan sanarwa a dukkanin kotunan kasar a yau Talata.

Kafin wannan doka, ana aurar da kananan yara mata sosai a Saudiyya, wadanda bas u kai shekaru 18 ba.

Daya yau kuma wannan doka ta sanar da cewa mutum ba zai tashi yay i aure ba, kuma uba ba zai tashi ya aurar da ‘yar sa ba, ko da ta cika shekaru 18, har sai ya je kotu, ya cika sharuddan da aka gindaya.

Wadannan sharudda duk su na kunshe cikin wannan sabuwar doka ta Haramta Aurar da Kananan Yara Mata a Saudiyya.

A cikin watan Janairu dai an fito da dokar da ta haramta aurar da yarinya ‘yar kasa da shekaru 15.

Amma kuma wannan sabuwar doka, ta maida shekarun wajibcin auren budurwa a Saudiyya, daga 15 zuwa 18.

Shekaru uku kenan kasar Saudiyya na ta bijiro da sabbin abubuwan da a baya aka haramta a kasar.

A Saudiyya cikin shekarar da ta gabata an amince mata su tuka mota, su shiga silima, kuma an amince a bude gidan rawa da gidan karta.

Share.

game da Author